Paul Kagame, shugaban kasar Rwanda, ya yaba wa kasar Sin, a taron dandalin tattaunawa na Doha, da ya gudana a kasar Qatar, a farkon watan nan da muke ciki. Inda shugaban ya ce, tasowar kasar Sin a duniya dama ce mai kyau ga kasashe masu tasowa, ganin yadda hadin gwiwar da suke yi tare da Sin ke haifar da alfanu ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki.
Sai dai kafin na ga rubutaccen bayani na jawabin shugaban, na ga labari mai alaka da batun, da kafar watsa labarai ta VOA ta kasar Amurka ta gabatar. Inda a kan shafin yanar gizo na VOA, an rubuta maganar da shugaba Kagame ya fada, kana a dab da zancen, an sanya alamar sokewa mai launin ja, gami da rubuta cewa “Kuskure ne”. Sa’an nan a cikin bayanin da ta wallafa, VOA ta zargi shugaba Kagame da “murde gaskiya”, kana ta ambaci dimbin laifuka na wai “tarkon bashi”, da “kwace damar yin aiki na ‘yan Afirka”, da “keta hakkin dan Adam”, da dai sauransu, wadanda kafofin yada labaru na kasashen yamma su kan dora wa kasar Sin.
- Noman Zamani: Jigawa Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanin CAMCE A Birnin Beijing
- ‘Yan Bindiga Sun Ƙwace Kayan Abincin Kirsimeti A Kaduna
Amma a hakika, wani abu da VOA din ba ta ambata shi ne, yayin da shugaba Kagame ke jawabi a wajen wani taro a karkashin dandalin Doha, wani shugaba na daban daga nahiyar Afirka na tare da shi, wato shugaban kasar Namibia Nangolo Mbumba. Sa’an nan a cikin jawabinsa, shugaba Mbumba shi ma ya yi wa kasar Sin yabo, kan yadda ta yi kokarin tabbatar da amfanawa dukkan bangarori, yayin da take hadin kai da sauran kasashe. To, watakila a ganin VOA, wannan shugaba na Afirka shi ma yana “murde gaskiya”? Watakila VOA din za ta sanya karin wata alamar sokewa mai launin ja a shafinta na yanar gizo?
Sai dai wani rahoton da cibiyar nazarin manufofi ta kungiyar Asiya, dake birnin New York na kasar Amurka, ta gabatar a farkon watan nan, ya nuna cewa, kasar Sin tana samu karbuwa a tsakanin al’ummun kasashen Afirka, saboda a ganinsu kasar Sin ta samar da damammaki na raya tattalin arziki ga nahiyar Afirka. An ce ko a kasar Eswatini, wata kasar da ba ta kulla huldar diplomasiyya tare da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ba tukuna, al’ummarta su ma suna amincewa da kasar Sin sosai, inda kaso 73% cikin jama’ar kasar ke ganin cewa, ayyuka masu alaka da tattalin arziki da kasar Sin ke aiwatarwa na haifar da tasiri mai yakini kan ci gaban tattalin arzikin kasarsu.
To, idan ka tambayi ra’ayina dangane da batun, zan ce, sam ban yi mamaki ba, kan goyon bayan da al’ummun kasashen Afirka ke nunawa kasar Sin. Saboda na san ka’idar tushe ta gwamnatin kasar Sin a fannin hulda da kasashen Afirka ita ce, nuna gaskiya, da kauna, da sahihanci, da samar da takamaiman alfanu ga jama’ar kasashen Afirka.
A ganina, bai kamata kafofin watsa labarai na kasashen yamma su wuce gona da iri a yunkurinsu na shafa wa kasar Sin kashin kaza ba, har ma sun dora wa shugaban wata kasa laifi, da sanya alamar sokewa mai launin ja a dab da maganarsa, cikin matukar fushi. Kana zan ba su karin magana guda 2 a matsayin abun tunasarwa, wato: “Hanyar gaskiya ba kaya.” Kana, “kowa ya yi karyar dare, gari ya waye.” (Bello Wang)