Yana daga cikin dabi’u na mata, neman hanyar da za su mallaki miji. Irin wannan lamari kan ba wasu matan matsala wajen gane yadda za su bi su mallaki miji cikin sauki. Wasu daga ciki gani suke zuwa wurin boka ko malam a samu wasu siddabaru a matsayin taimako domin mallake miji shi ya fi sauki.
Wasu su kan dace a hakan, wasu kuma akasin haka ne. Ga wadanda suka yi dace siddabarun ya yi masu amfani, zuwa wani dan lokaci kalilan zai daina amfani a koma kiyayya.
- Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
- An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jam’iyyar ADC Kan Shugabancin David Mark
Mata ga hanya mafi sauki wajen mallakar miji wanda aka tsara bisa koyarwa manzo. Kamar yadda malamai na addini ke nasiha da tuni kan cewa, Aljannar mace na karkashin kafar mijinta. Kawai ki dukufa kan wadannan ababe da ma wasu don mallakar miji cikin sauki:
(1)Ya kasance duk magana da za ta fita daga bakinki mai dadi ce a kunnen mijinki wadda za ta sa shi murmushi da jin dadi.
(2) Ki kasance mai sakin fuska ga mijinki a duk lokacin da ya shigo gida ya same ki cikin farinciki ko da akasin haka ne.
(3)Ki kasance a kullum kin dauki mijinki tamkar sarki ne ta wurin mutunta shi, da juriya wajen daukar laifinsa ya dawo kanki saboda bashi girma ko da ke ce da gaskiya.
(4)Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi shi ne kofa na kowane sharri.
(5) Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai saba wa addini ba ki yi masa.
(6) Ki nuna wa mijinki komai naki nashi ne komai nashi kuma naski ne, ki nuna baki da iko a kai sai abin da ya yi. 7. Ki kasance mai kula da abubuwan da yake dubawa bayan kin yi kwalliya. Kuma kin tabbatar duk lokacin da ya dawo yana neman buta ne, to ki kula da sanya ruwa a cikin butar.
(8) Ki kasan ce mai yawan godiya kan duk abin da ya kawo miki gida komai kankantarsa kar ki raina, sannan ki nuna masa kokarinsa. 9. Kar ki sake ko ki yi kasa a gwiwa wajen girmama duk wadanda kika san yana girmama su, kama daga iyaye har ‘yan uwa da abokan arzikinsa.
(10) Kar ki yawaita tambayarsa daga ina kake ko me kake yi sai yanzu kake dawowa? Ki kasance mai boye sirrinsa wajen iyayenki da sauran al’umma. 11. Kar ki yarda duk lokacin da ya kira ki ki kawo masa wani abu ki tura wani ko wata ta kawo, ki je ki yi da kanki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp