• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

by Leadership Hausa and Sulaiman
23 seconds ago
in Adon Gari
0
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu. Jama’a barkanmu da sake kasancewa tare da wannan fili mai albarka, wanda yake zakulo muku batutuwan da suke ci mana tuwo a kwarya, musamman a wannan zamani da muke ciki.

A daidai wannan lokaci, zan yi magana ne a kan aure, idan muka yi duba za mu ga cewa; a Arewacin Nijeriya ne aka fi samun mace-macen aure, amma kusan na ce mutanenmu hankalinsu bai kawo kai ba, mene ne ya sa?

 

Mene ne kuma dalili?

Magana ta gaskiya matsala daya ce zuwa biyu ko uku, na farko akwai laifin iyaye, na biyu akwai laifin samari da suke zuwa su yi auren, na uku kuma akwai laifin amaryar wacce ita ce take zaman auren.

Labarai Masu Nasaba

Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure

Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?

Bari na fara da maganar farko, dalilin da ya sa na ce laifin iyaye ne shi ne; duk mutumin da ya zo zai auri ‘yarka, idan kana da ‘ya ta isa aure, ya kamata ka zaunar da shi ka tambaye shi; mene ne ma auren, kuma me yasa yake son ya auri ‘yar taka? Da yawan samarin da suke yin aure, ba su san ma mene ne auren ba.

Alal hakikanin gaskiya, sha’awa ce kawai take tunzura su; a tunanin samari jima’i kawai shi ne aure, wannan shi yake kawo mace-macen aure ka ga namiji ya saki mace cikin sauki. Domin idan don sha’awa ka yi, da zarar ka gusar da sha’awarka za ka ji to, ai ba ka da kuma wata bukata a wajenta.

Don haka, yana da kyau ka tambayi wanda ya zo neman auren ‘yarka cewa; mene ne ma auren? a nan za ka gane ko yana da addini ko kuma ba shi da shi, ya san mene ne ma auren ko bai sani ba, shin ya san aure sunnah ce ta Ma’aiki ko ma bai sani ba?

Ba fa jima’i ne kawai aure ba, wani sha’awa ce, rudu ne kawai tana da kyau, ta iya kwalliya da dai sauransu, shikenan da an yi auren kuma ya ga ta zo ta yi wanka ta yi kaza, ya ga ta tashi daga barci, ya zo ya same ta ba wanka, sai ya ga kamar ba waccan ba ce, to ya kamata ya san ma mene ne auren tukunna.

Ba laifi ba ne, kuma ba abin kunya ba ne, ka sanar da shi kai da shi, domin burinka idan ya auri ‘yarka su zauna har abadan da’iman mutu-ka-raba, ba kawai a yi rawar kafa ba. Ah! kawai shikkenan yarinyar nan duk kannenta sun yi aure ga wani ya fito kawai sai a ce turo iyayenka, saboda me, waye shi, mene ne matakin iliminsa, me ya sani, me ya sani dangane da auren?

Sannan ku zaunar da ‘yarku, ku sanar da ita mene ne aure, da kike ta rawar kafa za ki auri wane, me ya sa kike sonsa? Don haka, ga abin da addini ya shara’anta, ga abin da ya kamata ki yi idan kina son ki zauna lafiya, ga kuma yadda ya kamata ki yi.

Neman kai kake da ‘yarka? lokacin da ka yi aure ka haife ta har ta yi laulayi aka goya ta, ta tashi ta fara rarrafe, ka raine ta, makaranta safe, rana da kuma dare, ka kai ta ka dauko ta, duk ba ka yi neman kai da ita ba sai da aka zo dan taki na ‘yan shekaru kawai da wani yake so, kake son ya aure ta sai ka yi ta gaggawa?

Duk mace a duniya Allah ya rubuta mata mijinta, amma dolenmu sai mun tsaya mun mika wa Allah lamarinmu, ba lallai sai maikudi za ki aura ki zauna lafiya ba, Hajiya ki nemi mai rufin asiri, wanda za ku zauna lafiya ya rufa miki asiri ya ga mutuncin iyayenki, ya kare ki, ya kare mutuncinki, ya kuma kare addininki.

Sannan su ma na dawo kan su samarin masu yin aure, sha’awa ce take sa wa da yawa muke yin aure, ko kuma tana burge ni, ko abokina ya auri wata kyakkyawa fara kal ni ma kal zan aura a ce shege wane ya auri wance, “Kai! ka ga matar wane?”, wa ya aike ka Alaji duk ga abin da Annabin tsira ya karanto ka kalli wannan suffofin shin tana daga ciki?

Amma ba ma bi, muna dauka ne kawai mai kyau ce, ta iya wanka, ta iya girki, “kai! ka ga idan ta yi wanka, ai idan na auri wannan ai na kece a cikin abokanai”, wa ya fada maka? ba wannan ba ne Alaji.

Alaji ka yi aure kai kwanciyar hankali, ka bi abin da addini ya ce da abin da ma’aiki (SAW) ya fada, ga irin tsarin duk ya zayyano mana siffofi.

Idan za ka auri mace, kar ka yi mata karya, ku yi gaskiya da gaskiya, kuma ka sanar da ita ga irin zaman da kake so ku yi tun kuna waje, yadda idan ta shiga ma ba za ta ga ka yi mata karya ba, Alaji wallahi idan ka yi karya ma ba za ka ga daidai a gidanka ba, ka yi iya bakin ikonka kar ka kwaikwayi rayuwar wani ka yi iya irin taka wacce ba ta kaucewa al’ada da addininmu na musulunci ba.

Idan muna so a rage zawarawa da mace-macen aure, to kafin auren sai mu rika kiyayewa da sanin me ya kamata mu yi.

Wassalamu Alaikum.

Daga Ibrahim Bala


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

Related

Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure
Adon Gari

Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure

2 months ago
Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?

3 months ago
Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi
Adon Gari

Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi

6 months ago
Mata Mu Dage Da Neman Ilimi Da Neman Na Kanmu -Hassana Umar
Adon Gari

Mata Mu Dage Da Neman Ilimi Da Neman Na Kanmu -Hassana Umar

6 months ago
Mata Ku Dage Da Karatu Domin Tallafa Wa Rayuwarku Da Ta ‘Ya’yanku – Zahra’u Adam
Adon Gari

Mata Ku Dage Da Karatu Domin Tallafa Wa Rayuwarku Da Ta ‘Ya’yanku – Zahra’u Adam

7 months ago
Nijeriya Da Brazil Sun Cimma Yarjejeniyar Bunkasa Noman Zamani A Kasar Nan
Adon Gari

Halima Aliko Dangote Ta Nemi A Ba Mata Damar Shiga Harkokin Kasuwanci Yadda Ya Kamata

7 months ago

LABARAI MASU NASABA

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

July 27, 2025
aure

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

July 27, 2025
Yadda Ake Faten Acca

Yadda Ake Faten Acca

July 27, 2025
Hanyoyin Gyaran Gashi

Hanyoyin Gyaran Gashi

July 27, 2025
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.