Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanmu da sake kasancewa tare da wannan fili mai albarka,
wanda yake zaƙulo muku batutuwan da suke ci mana tuwo a ƙwarya, musamman a wannan zamani da muke ciki.
A daidai wannan lokaci, zan yi magana ne a kan aure, idan muka yi duba za mu ga cewa; a Arewacin Nijeriya ne aka fi samun mace-macen aure, amma kusan na ce mutanenmu hankalinsu bai kawo kai ba, mene ne ya sa?
Mene ne kuma dalili?
Magana ta gaskiya matsala daya ce zuwa biyu ko uku, na farko akwai laifin iyaye, na biyu akwai laifin samari da suke zuwa su yi auren, na uku kuma akwai laifin amaryar wacce ita ce take zaman auren.
Bari na fara da maganar farko, dalilin da ya sa na ce laifin iyaye ne shi ne; duk mutumin da ya zo zai auri ƴarka, idan kana da ƴa ta isa aure, ya kamata ka zaunar da shi ka tambaye shi; mene ne ma auren, kuma me yasa yake son ya auri ƴar taka? da yawan samarin da suke yin aure, ba su san ma mene ne auren ba.
Alal haƙiƙanin gaskiya, sha’awa ce kawai take tunzura su; a tunanin samari jima’i kawai shi ne aure, wannan shi yake kawo mace-macen aure ka ga namiji ya saki mace cikin sauƙi. ɗomin idan don sha’awa ka yi, da zarar ka gusar da sha’awarka za ka ji to, ai ba ka da kuma wata buƙata a wajenta.
ɗon haka, yana da kyau ka tambayi wanda ya zo neman auren ƴarka cewa; mene ne ma auren? a nan za ka gane ko yana da addini ko kuma ba shi da shi, ya san mene ne ma auren ko bai sani ba, shin ya san aure sunnah ce ta Ma’aiki ko ma bai sani ba?
Ba fa jima’i ne kawai aure ba, wani sha’awa ce, ruɗu ne kawai tana da kyau, ta iya kwalliya da dai sauransu, shikenan da an yi auren kuma ya ga ta zo ta yi wanka ta yi kaza, ya ga ta tashi daga barci, ya zo ya same ta ba wanka, sai ya ga kamar ba waccan ba ce, to ya kamata ya san ma mene ne auren tukunna.
Ba laifi ba ne, kuma ba abin kunya ba ne, ka sanar da shi kai da shi, domin burinka idan ya auri ƴarka su zauna har abadan da’iman mutu-ka-raba, ba kawai a yi rawar ƙafa ba. Ah! kawai shikkenan yarinyar nan duk ƙannenta sun yi aure ga wani ya fito kawai sai a ce turo iyayenka, saboda me, waye shi, mene ne matakin iliminsa, me ya sani, me ya sani dangane da auren?
Sannan ku zaunar da ƴarku, ku sanar da ita mene ne aure, da kike ta rawar ƙafa za ki auri wane, me ya sa kike sonsa? ɗon haka, ga abin da addini ya shara’anta, ga abin da ya kamata ki yi idan kina son ki zauna lafiya, ga kuma yadda ya kamata ki yi.
Neman kai kake da ƴarka? lokacin da ka yi aure ka haife ta har ta yi laulayi aka goya ta, ta tashi ta fara rarrafe, ka raine ta, makaranta safe, rana da kuma dare, ka kai ta ka dauko ta, duk ba ka yi neman kai da ita ba sai da aka zo dan taƙi na ƴan shekaru kawai da wani yake so, kake son ya aure ta sai ka yi ta gaggawa?
ɗuk mace a duniya Allah ya rubuta mata mijinta, amma dolenmu sai mun tsaya mun miƙa wa Allah lamarinmu, ba lallai sai maikuɗi za ki aura ki zauna lafiya ba, Hajiya ki nemi mai rufin asiri, wanda za ku zauna lafiya ya rufa miki asiri ya ga mutuncin iyayenki, ya kare ki, ya kare mutuncinki, ya kuma kare addininki.
Sannan su ma na dawo kan su samarin masu yin aure, sha’awa ce take sa wa da yawa muke yin aure, ko kuma tana burge ni, ko abokina ya auri wata kyakkyawa fara ƙal ni ma ƙal zan aura a ce shege wane ya auri wance, “Kai! ka ga matar wane?”, wa ya aike ka Alaji duk ga abin da Annabin tsira ya karanto ka kalli wannan suffofin shin tana daga ciki?
Amma ba ma bi, muna dauka ne kawai mai kyau ce, ta iya wanka, ta iya girki, “kai! ka ga idan ta yi wanka, ai idan na auri wannan ai na kece a cikin abokanai”, wa ya fada maka? ba wannan ba ne Alaji.
Alaji ka yi aure kai kwanciyar hankali, ka bi abin da addini ya ce da abin da ma’aiki (SAW) ya fada, ga irin tsarin duk ya zayyano mana siffofi.
Idan za ka auri mace, kar ka yi mata ƙarya, ku yi gaskiya da gaskiya, kuma ka sanar da ita ga irin zaman da kake so ku yi tun kuna waje, yadda idan ta shiga ma ba za ta ga ka yi mata ƙarya ba, Alaji wallahi idan ka yi ƙarya ma ba za ka ga daidai a gidanka ba, ka yi iya bakin ikonka kar ka kwaikwayi rayuwar wani ka yi iya irin taka wacce ba ta kaucewa al’ada da addininmu na musulunci ba.
Idan muna so a rage zawarawa da mace-macen aure, to kafin auren sai mu riƙa kiyayewa da sanin me ya kamata mu yi.
Wassalamu Alaikum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp