ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, Sin tana kokarin gina layukan dogo a kasashen nahiyar Asiya, da Turai, da arewacin Amurka, da kuma Afirka, wadanda suka zama shaidun aikin raya shirin “ziri daya da hanya daya” da kuma hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. 

Wang Wenbin ya bayyana yayin taron manema labarai na jiya cewa, hanyoyin jiragen kasa dake tsakanin Mombasa da Nairobi na kasar Kenya sun sa kaimi ga raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da kuma kyautata zaman rayuwar jama’a a kasar Kenya. Shekaru biyar bayan fara zirga-zirgar jiragen kasa, yawan tikitin kujerun jiragen kasa da aka sayar ya zarce kashi 90 cikin dari. Kana bisa kididdigar da aka yi, yawan kudin da layukan dogo suka samu, ya zarce kashi 2 cikin dari bisa yawan GDP na kasar Kenya, kana sun samar da ayyukan yi kimanin dubu 50, tare da horar da kwararru fiye da 1700 a fannin ilmin hanyoyin jiragen kasa da sarrafa hanyoyin jiragen kasa a kasar Kenya.
Wani rahoton jaridar The Daily Telegraph ta kasar Birtaniya, ya sanya layin dogon dake tsakanin Mombasa da Nairobi a matsayin daya daga cikin manyan layukan dogo mafi samun karbuwa guda 13 a duniya.

Kafar yawon shakatawa ta kamfanin dillancin labaru na CNN ya bada shawara ga masu yawon shakatawa kan muhimman abubuwa 20 da aka fi yi a kasar Kenya, inda hawa jirgin kasa tsakanin Mombasa da Nairobi ya kasance a matsayi na biyar. Kamar yadda shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi ya samar da kyakkyawar makoma ga dukkan mutanen kasar a fannonin samun ayyukan yi da wadata.

ADVERTISEMENT

Wang Wenbin ya kara da cewa, wannan lamari na shaida cewa, ya kamata a yi hadin gwiwa da samun moriyar juna da adalci da wadata tare, wanda zai sa kaimi ga bunkasa dukkan sassan duniya baki daya.

Ya ce Sin za ta ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban don sa kaimi ga raya shirin “ziri daya da hanya daya” da bayar da gudummawa ga samun ci gaba da wadata na bai daya a duniya. (Zainab)

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow
Daga Birnin Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa - Atiku

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.