Biyo bayan samun wasu cututtukan da ke kara jawo raguwar samun girbi mai yawa a wannan nazari, an samar da wasu muhimman matakai guda hudu da manoma za su kare amfaninsu daga wannan bazarana.
Ana so manomi ya fahimci cutar: Bullar cutar da ke yi wa amfanin gona illa, ta kan sha banban daga shekara zuwa shekara; wanda kuma ake so manoma a koda-yaushe su rika kasancewa a ankare, don sanin wace sabuwar cuta ce za ta iya bulla.
Misali, idan a kan ganyen Dawa ta bulla, ganyen zai koma tsanwa ko kuma alamar gansa-kuka.
Tsallake siradin cutar: Manoma za su iya tsallake wannan siradi ne ta hanyar lura da nau’in cutar da ka iya harbin jijiyar amfanin da suka shuka.
Misali, sauyin yanayi a fannin noman Dawa, zai iya jawo yaduwar cutar, saboda haka ba a so manomi ya yi sako-sako a dukkanin kakar noma koda kuwa, an samu ruwan sama mai yawa.
Samun bullar wannan cuta, kan iya yi wa amfaninin manomi illa matukar bai mayar da hankali kan amfanin da ya shuka ba.
Shiga cikin filin gona a kan lokaci: Idan manoma suka shiga filin gonar da za su yi shuka a kan lokaci, hakan zai ba su damar daukar matakan gaggawa; ta hanyar sanin kowace irin cuta ce, da za ta yi wa amfaninsu illa tare da sanin wane irin magani ya fi dacewa su yi amfani da shi.
Ana kuma bukatar manomi ya tabbatar yana auna kimar amfanin da ya shuka, duba da cewa; cutar da ke lalata amfanin za ta iya bulla a wani yanayi na daban.
Haza zalika, fara bayyanar matsala a Jijiyar amfani na nuna alamar cewa, wata cuta ta bulla; misali jijiar za ta fara lalacewa.
Fahimtar mahimmanci yin amfani da maganin kashe cutar: Yana da kyau manomi ya fahimci muhimmancin amfanin da maganin da zai kashe cutar.
Magance cutar da ke bijere wa magani: Yana da matukar kyau, manomi ya tabbatar ya sa a zuciyarsa cewa; abu na farko da zai yi shi ne, magance cutar da ke bijere wa magani, musamman wajen samun damar daukar matakin gaggawa a kanta.
Don haka, ana so manomi ya rika amafani da magungunan kashe wannan cuta da ke da inganci, wanda hakan zai taimaka masa wajen magance irin wadannan cututtuka masu bijire wa magani.