Talotalo daya ne daga cikin dabbobin da ake kiwo a gida. Ta dara kaza girma, shi ya sa wasu suka fi son ta saboda yawan nama fiye da kaza. Har ila yau, masu kiwon talotalo sun fi morewa fiye da masu kiwon kaji saboda an fi samun riba da su musamman ga wanda ya raine su tun suna kanana.
1- Nau’in Abincin Talatalo: Talotalo, ba kawai kayan ganye ko ciyawa da sauran kayan lambu yake ci ba, yana kuma cin nama da sauran kwari da suka hada da Tana da sauran makamantansu.
- Yawan Kudin Cinikin Samar Da Hidima Na Shigi Da Fici A Farkon Rabin Bana A Kasar Sin Ya Karu Da 14%
- Yadda Aljanu Suka Shiga Zanga-zangar Da Aka Yi A Kano – Dakta Kachako
Sai dai, masu bukatar cin namansu, sun fi son masu kiwon su; su ciyar da su da sauran kayan lambu, wanda hakan ya sa masu kiwon, kara kayan lambu a cikin nau’in abincin ciyar da su, domin samun biyan bukatar masu saya; don cin namansu.
Kazalika, wasu nau’ikan Talotalon, ba a ciyar da su da nama da sauran kwari, duk da cewa; matansu na da bukatar cin su.
2- Ba lallai sai ga masu kiwon su ba, ana iya daukar kimanin tsawon kwana 365 ga masu masha’awar kiwata su, kafin su kai munzalin girma, sannan ana bukatar a rika duba lafiyarsu tare da zuba musu magunguna a cikin abincinsu.
3- Lokacin da gashinsu ke fara zubewa: A yayin da suke kanana, gashinsu ke fara zubewa; sai kuma gashin fara girma ya fara fito musu.
4- Wasu nau’ikan Talotalo na son junansu, wasu kuma ba su cika son ‘yayan nasu ba: Ko da an samar wa da Talotalo wadataccen filin da za su yi kiwo, duk da hakan; su kan kasance kusa da junansu, saboda wayewar da suke da ita.
Idan ma har wani yabi ta tsakiyarsu a lokain da suke kusa da junansu, za su sake dawowa wuri daya su hade da junansu.