Abba Ibrahim Wada" />

Har Yanzu Ba Mu San Darajar Maki Uku Ba – Lampard

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Frank Lampard, ya bayyana cewa har yanzu ‘yan wasan kungiyarsa basu san darajar maki uku ba a wasa kuma yarinta tana cigaba da bibiyar tunaninsu.

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta doke Chelsea a mintin karshe na wasan firimiya mako na 23 da kungiyoyin suka fafata a filin wasa na St James Park duk da cewa Chelsea tafi mallakar kwallo a fafawar.

Chelsea ce dai ta rike mafi yawan wasan amma hakan bai sa tawagar Lampard din ta ci kwallo ba duk da irin hare-haren da ‘yan wasan kungiyar suka kai sai dai duk da haka Lampard ya kalubalanci ‘yan wasan nasa.

Dan wasan gaba, Tammy Abraham ya buga kwallo waje daga gefen turke sannan mai tsaron raga Martin Dubrabka ya bige harin da N’golo Kante ya kai masa kusan wadannan sune hare-hare masu muni da Chelsea ta kai.

Kafin a ci kwallon, masu masaukin bakin ne Newcastle suka kusa jefa kwallo a raga lokacin da Joelinton ya bugo turke da kwallon da ya saka wa kai a minti na 22 sai dai daga baya kuma suka cigaba da kai hari.

Frank Lampard ya bayyana cewa wasu lokutan ‘yan wasan nasa suna nuna yarinta sosai saboda idan akaje mintin karshe idan har baka iya cin kwallo da yawa ba dole sai kana kula da ragarka saboda kada a karshe ayi maka illa kuma hakan yana nuna cewa ‘yan wasan kungiyar basu san darajar maki uku ba.

Exit mobile version