CRI Hausa" />

Har Yanzu Kasar Sin Kasa Ce Dake Jawo Jarin Waje Sosai

Bisa kididdigar da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayar a yau Alhamis, an ce, a cikin farko watanni 5 da suka gabata na bana, yawan jarin waje da aka yi amfani da shi a kasar Sin ya kai kimanin kudin RMB yuan biliyan 369, wato ya karu da kaso 6.8%, bisa makamancin lokaci na bara. A lokacin da yawan jarin waje da ake zubawa a duk fadin duniya yake raguwa, jarin waje da aka zuba a kasar Sin ya alamta cewa, har yanzu kasar Sin kasa ce da aka fi son zuba jari. Ko shakka babu, maganar wai “kamfanoni masu jarin waje za su kaura daga kasar Sin, sakamakon karin harajin kwastam da ake bugawa” ba shi da tushe ko kadan. Sannan an musanta magana cewa wai tattalin arzikin kasar Sin yana lalacewa sabo da karin jarin waje da ake zubawa a kasar Sin.
Yanzu kasar Sin na kokarin inganta yanayin tattalin arziki, ta yadda za ta iya ci gaba da jawo hankulan kamfanoni masu jarin waje da su zuba karin jarinsu a kasar.

Idan an dudduba jarin waje da aka zuba a kasar Sin a cikin farkon watanni 5 da suka gabata na bana, za a iya ganin halaye 2, wato, yanzu baki ’yan kasuwa na kokarin zuba jari a masana’antun fasahohin zamani a nan kasar Sin, maimakon hada-hadar wasu kayayyaki kadai. Bugu da kari, jari daga yankin Hongkong na kasar Sin da kasashen Koriya ta kudu da Japan, da Amurka, da Burtaniya, da Jamus, da kungiyar EU, suna ta karuwa. Alal misali, jarin da baki ’yan kasuwa na Amurka suka zuba a kasar Sin ya karu da 7.5% bisa makamancin lokacin bara. Wadannan alkalumai sun shaida cewa, maganar wai “kamfanoni masu jarin waje za su kaura daga kasar Sin sakamakon karin harajin kwastam da ake bugawa” ita ma karya ce kawai.
Dalilin da ya sa bangaren Amurka ya kan fitar da batun wai “kamfanoni masu jarin waje za su kaura daga kasar Sin sakamakon karin harajin kwastam da ake bugawa” shi ne, yana son yin amfani da ayyuka daban daban da ake rarraba wa masana’antu daban daban na kasashen duniya, wajen lalata tattalin arzikin kasar Sin, amma a hakika dai, bai san aihinin halinsa ba.
Bari mu ba da misali kan yadda aka kaurar da sana’ar yadi, da tufafi a fadin duniya. A cikin shekaru 70 da suka gabata, an kaurar da wannnan sana’a daga Amurka zuwa Japan, sai kuma daga Japan zuwa yankunan Asiya hudu mafi karfin tattalin arziki, daga bisani kuma, zuwa kasar Sin. Har wa yau zuwa kasashen gabas maso kudancin Asiya da Afrika. Wannan sauyi ya dace da tsarin bunkasuwar tattalin arziki, babu ruwan haraji da aka kara kakabawa ko kadan.
Amurka na yunkuri shafa kashin kaji kan tattalin arzikin kasar Sin da zummar matsin lamba mai tsanani a kanta, har ma ta kirkiro wasu karairayi marasa tushe. Alal misali, ta ce wai gwamnatin Amurka ta tilasta kasar Sin da ta yi hasarar kudi har dala triliyan 1.5 zuwa 2, kafofin yada labarai na Amurka na zargi wannan zance cewa, yawan kudin dake shafar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kimanin triliyan 1.3, hasarar da take yi bai kamata ta yi sama da wannan adadi ba. A hakika dai, Sin tana da karfin sarrafa hasarorin da takaddamar dake tsakanin kasashen biyu ke jawo mata, a maimakon haka, Amurka ta yi asara mafi tsakani. Yawan karin mutane da suka kama aiki ba na aikin gona ba, ya kai dubu 75 kawai a watan Mayu da ya gabata, wanda bai kai rabin adadin da aka hasashe ba. IMF ta ba da wani rahoto a karshen watan Mayu cewa, yawan karin kudin da aka kashe don haraji da Amurka ta kara kakabawa kasar Sin, yawancinsu kamfanonin Amurka suka biya su.

Ban da wannan kuma, kungiyar UNCTAD ta ba da kididdigar cewa, jimilar FDI, wato yawan jarin da wata kasa ta jawo daga ketare ya ragu da kashi 13 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, daga cikinsu wannan adadi a Amurka ya kai kashi 9 cikin dari, a maimakon haka, wannan adadi ya ragu da kashi 4 cikin dari a kasar Sin. A cikin farkon watannin 5 da suka gabata, yawan jarin da kasar Sin ta jawo daga ketare ya rika karuwa, inda ya kai kashi 6.8 cikin dari, abun da ya shaida cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai inganci, na da babban karfi wajen jawo hankalin jarin ketare.
Dalilin da ya sa kasar Sin ke iya janyo jari daga kasashen waje, shi ne domin kasar ta mallaki cikakken tsarin da ya shafi dukkan sana’o’i a cikin gida, da tsarin jigilar kaya cikin sauki, da dimbin kwararru a fannoni daban daban, gami da kwarewa a fannin samar da sabbin fasahohi. Duk wadannan abubuwa sun rage kudin da kamfanonin ketare ke kashewa, gami da taimakawa wajen samar da sabbin fasahohi don raya tattalin arzikin kasar.
Sa’an nan wani abun da ya fi muhimmanci shi ne, babbar kasuwar kasar da ta kunshi mutane kimanin biliyan 1.4, tana taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da tattalin arzikin kasar gaba. Yadda ake kokarin inganta tsarin tattalin arzikin kasar, gami da sayen karin kayayyaki masu inganci, sun ba ’yan kasuwan kasashen waje damar samun makudan riba a kasar. Alal misali, a shekarar 2017 kadai, kamfanonin kasar Amurka dake zuba jari a kasar Sin sun samu kimanin dalar Amurka biliyan 700 daga kasuwar kasar Sin. Ganin wannan babbar riba, ko akwai wani kamfanin da zai iya kin zuba jari a kasar Sin, da nisantar kasuwar kasar? Hakan ba zai yiwu ba.
Sabo da haka, duk da cewa kasar Amurka ta yi ikirarin cewa, wai “kamfanoni masu jarin waje za su kaura daga kasar Sin sakamakon karin harajin kwastam da ake bugawa”, amma a hakika an ga yadda manyan kamfanonin kasashe daban daban ke kokarin zuba karin jari a kasar Sin. Misali an fara gina wata babbar ma’aikata ta kamfanin Tesla na kasar Amurka a birnin Shanghai na kasar Sin, sa’an nan kamfanin British Telecom ya zama kamfanin sadarwa na ketare na farko da ya samu izinin samar da hidima a wurare daban daban na kasar Sin.
A nasu bangaren, kamfanin Qualcomm, da OSI Group, na kasar Amurka, da Jaguar Land Rover Corporate din kasar Birtaniya, da Schneider Electric na kasar Faransa, dukkansu sun sa niyyar habaka ayyukansu a kasar Sin.
Yanzu ko da yake takaddamar ciniki da kasar Amurka ta tayar da ita, ta haifar da wani yanayi na rashin tabbas ga tattalin arzikin duniya, da sabbaba raguwar jarin da ake zubawa kasashen waje, amma duk da haka, kasar Sin na kokarin bude kofarta ga kasashen waje, da yin amfani da jarin waje yadda ya kamata, da kokarin kare hakkin kamfanonin ketare, ta samar da hidima mai inganci ga kamfanoni masu jarin waje. Ta wadannan matakai, kasar Sin na shaida wa duniya cewa, ita wata aminiya ce da za a iya dogaro da ita. (Masu Fassarwa: Sanusi Chen, Amina Xu, Bello Wang, ma’aikatan CRI Hausa)

Exit mobile version