Minna, " />

Har Yanzu Ma’aikatan Kananan Hukumomin Neja Ba Su San Matsayin Albashin Watan Maris Ba

A dai-dai lokacin da aka shiga rana ta goma da kafa dokar ta baci a Neja kan annobar COVID-19 wanda ya tilasta rufe kasuwanni da ma’aikatun gwamnatin jiha da gwamnatin ta kakabawa al’ummar jihar a shirin ta na dakile cutar daga yaduwa a jihar, Ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makarantar faramare sun fara kokawa kan rashin biyan su albashin watan Maris da gwamnatin ta kasa yi zuwa yanzu.

Wani shugaban makarantar faramare na gwamnatin jiha da ya nemi a sakaya sunan sa yace a gaskiya suna cikin halin kunci tare da iyalan su wanda ba su san ranar da gwamnatin ta shirya biyan su albashin su na watan da ya gabata ba, idan ana cewar annobar COVID-19 ta sanya aka kakaba wannan dokar, shin ita din ce ta hana biyan su hakkin su alhalin an biya ma’aikatan jiha.

Ya kamata ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu ta sakar wa kananan hukumomi kudaden su dan biyan ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makaranta, saboda halin da suke ciki na rashin abinci a gidajen su. Muna da iyali kamar kowa, an biya ma’aikatan jiha, an biya ‘yan siyasar jiha sai mu da ke karkashin kananan hukumomi ake takawa duk da cewar gwamnatin tarayya ta sakarwa kananan hukumomin kudaden su kamar yadda rahotanni suka tabbatar amma gwamnatin jiha tana kokarin zaunawa akan su.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewar daga cikin kudaden na kananan hukumomi, gwamnatin jiha na yunkurin zaftare kashi ashirin cikin dari wanda shugabannin kananan hukumomin ashirin da biyar ba su amince da hakan ba.

Rahotannin sun tabbatar da cewar zuwa yanzu duk da wannan yaki da dakile yaduwar annobar COBID-19 da jihar ke yi kungiyar kwadago na ma’aikatan kananan hukumomi NULGE da takwarata ta malaman makarantun faramare ,NUT na can na zama akan wannan lamarin.

Yunkurin jin ta bakin ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu ta jiha ya citura, kusan dukkanin ‘yan siyasar jihar da ke da kusanci da gwamnatin sun ki yarda su tofa albarkacin bakin su kan lamarin.

 

 

 

 

Exit mobile version