Daga Sulaiman Bala Idris
A ranar Juma’a 8 ga watan Satumba, 2017 ne kasar Amurka ta bayyana cewa har yanzun tattalin arzikin Nijeriya na fuskantar barazana, wanda ke da alaka da ayyukan tada kayar baya da ‘yan ta’addan Neja Delta ke yi, na tarwatsa bututun man fetur da ke yankin.
Wannan gargadi na kasar Amurka ya fito ne daga bakin Shugaban Hafsan Sojin Ruwan Amurka, mai lura da yankunan Turai da Afrika, Admiral Michelle Howard. A yayin kuma da gargadin ya zo daidai lokacin da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fid da rahoton da ke cewa Nijeriya ta fice daga matsin tattalin arziki da karin 0.55.
Howard, ya bayyana haka ne a lokacin da yake mika lambar yabo ga mataimakin wakilin sojin Nijeriya a Amurka, Kaftin Kolawole Oguntuda, a babban hedikwatar Sojin Ruwa da ke Abuja.
Ya ce: “Hakowa da cinikayyar man fetur ne kaso 75% da ke kawowa Nijeriya kudin shiga, don haka idan ya zama ana samun barazanar fasa bututu, da ayyukan tsagera a yankin Neja Delta, tattalin arzikin Nijeriya zai kasance cikin barazana.
“A irin wannan halin ne ake matukar bukatar aikin Sojin Ruwa. A matsayina na kwamanda, na dauki Sojin Ruwan Nijeriya a matsayin muhimmai kuma wadanda zasu iya taka muhimmiyar rawa wurin tabbatar da tsaro a yankin Afrika ta Yamma. Kuma zamu kara karfin alaka tsakanin rundunarmu da takwarorinmu na Afrika wurin wanzar da zaman lafiya.”
A yayin nasa jawabin, Shugaban Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya, Mataimakin Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas ya bayar da tabbacin cewa Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya a shirye suke domin fuskantar duk wata barazana da tsageran Neja Delta zasu yiwa Nijeriya.
“Ba sai wasu daga kasashen ketare sun fadi mana abin da ya kamace mu ba, ko yadda zamu magance duk wata barazana ko matsala da ke fuskantarmu da ma yankin Afrika ta Yamma.
“Tuni mun saba da ire-iren wadannan barazana da farmaki daga ‘yan fashi, da tsagera, musamman ma a shekarar bara. Haka kuma mun yi fama da barayin man fetur, da masu fasa bututu, har ma da masuntan da suke diban kifi a tekunmu ba tare da cika ka’ida ba. Don haka barazanar da kake cewa Nijeriya na fuskanta daga yankin Neja Delta. Zan so in tabbatar maka da cewa matukar mutum na raye, dole ne ya cigaba da ganin irin wannan rikice – rikice, sannan akwai hanyoyin magance wadannan matsaloli.” In ji Ibas