Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Har Yanzu Tsugune Ba Ta Kare Ba A Tsaron Jihar Katsina –Bincike

by Muhammad
February 10, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Jihar Katsina
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Awwal Jibril ‘Yankara,

Har yandu dai tsugune ba ta kare ba a kan lamarin tsaro a jihar Katsina, musamman a Kananan Hukumomin Faskari, Sabuwa da Dandume, inda kusan kullum sai an samu labarin garuruwan da ‘yan bindida suka shiga suka kashe Mutane, ko Suka kwashe su domin neman kudin fansa, ko suka kore dabbobin da Suka mallaka.

samndaads

Bincike sun nuna cewa garuruwa na baya-bayan nan da ‘yan bindigar Suka je, sun hada da Kauyan ‘Yar Daura da ke kusa da garin ‘Yankara, inda suka yi gaba da Mutum 11, dukkansu Mata, daga bisani suka nemi a ba su Naira Miliyan 10, bayan an cimma yarjejeniya, an biya su, kana suka sako su.

‘Yan bindigar sun je wasu garuruwan da suka hada da Unguwar Gizo, Unguwar Biri, Fankama, ‘Yar Itace, Tsuru, Mangorori, da sauransu, inda suka kore masu daruruwan shanu da tumakai, a wani garin ma har da kaji. ‘Yan bindigar sun kashe Mutane 10 a Unguwar Sarki, biyar a gidan Sarkin Makafi, Uku a Dankaya da wasu biyu a Jarkuka, duk a Karamar Hukumar Faskari.

A kwanaki biyu a jere, ‘yan bindigar sun kai hari a kauyukan ‘Yar Tasha, da Kwana Duke da ke Mazabar Tumburkai a Karamar Hukumar Dandume da kuma Doka da Garawa a Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna, inda Suka tafi da da mutane da dabbabo.Haka nan sun je kauyukan Dankaya, inda suka kashe Mutum uku, ciki har da jariri da Unguwar Hayaki a Mazabar Sheme ta Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.

Wannan na faruwa ne duk da dimbin jami’an tsaron da aka jibge a sansanin soja na Faskari, da ‘Yan Sandan kwantar da tarzoma da rundunar ‘Zaman Lafiya Dole’ ta Dan Zaki, yaran Marigayi Ali Kwara.

SendShareTweetShare
Previous Post

Hukumar Kwastom Ta Kama Haramtattun Kayayyakin Naira Miliyan 788 A Iyakar Seme

Next Post

Ku Shirya Jin Radadin Karin Farashin Fetur –Ministan Mai Ga ’Yan Nijeriya

RelatedPosts

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Daga Ahmed Muh'd Danasabe, Lokoja Ranar Lahadi da ta gabata...

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri Biyo bayan harin da mayakan Boko...

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Daga Musa Muhammad, Abuja An kammala dukkan shirye-shirye don fara...

Next Post
Farashin Mai

Ku Shirya Jin Radadin Karin Farashin Fetur –Ministan Mai Ga ’Yan Nijeriya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version