Amurka a makon da ya gabata ta dakatar da aika wa Isra’ila bama-bamai kan fargabar kai munanen hare-hare a Birnin Rafah da ke Kudancin Gaza, a cewar wani babban jami’in gwamnatin Amurka.
Jami’in ya shaida wa kafar yada labarai ta CBS cewa kayan sun hada da bam mai nauyin tan 1,800 2,000lb da 1,700 500lb.
- Kabilar Bayankole Da Innar Amarya Ke Jima’i Da Ango Domin Gwaji
- Ya Kamata Manchester United Ta Kori Erik ten Hag?
Ya kara da cewa Isra’ila ba ta saurari koken Amurka kan bukatun kayan agajin da suka kamata a kai wa mutanen Rafah ba.
Mai Magana Da Yawun Rundunar Sojin Isra’ila ta IDF Daniel Hagari ya shaida wa manema labarai cewa Amurka ta rika bayar da taimakon tsaro tun farkon yakin, inda ya kara da cewa an yi wata tattaunawar sirri tsakanin kasashen biyu.
Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a tsakiyar dare a zirin Gaza sa’o’i bayan sojojin Isra’ila cikin motocin yaki sun kwace mashigar Rafah da ke bangaren Falasdinawa a kan iyakar Masar.
Yanzu haka dai Isra’ila ta tsananta kai hare-hare a kewayen Rafah. Wasu kafofin sun ce mutum bakwai aka kashe ‘yan gida daya a wani hari da aka kai.
Rafah ta kasance muhimmiyar hanya ta shigar da kayan agaji kuma hanya daya da mutane ke iya fita daga garin tun farkon fara yaki tsakanin Isra’ila da Hamas a Oktoban shekarar da ta gabata.
An rufe mashigar tun safiyar ranar Laraba amma rundunar sojin ta ce za ta kara bude mashigar Kerem Shalom da ke kusa da wadda aka rufe tsawon kwanaki hudu.