Sanatoci 109 na Tarayyar Nìjeriya sun bayar da gudunmawar albashinsu na wata daya, wanda ya kai Naira Miliyan N109m ga iyalan wadanda harin Bam ya rutsa da su a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne ya bayyana hakan a gidan gwamnatin Kaduna a lokacin da ya jagoranci wata babbar tawaga ta majalisar zuwa jihar a ranar Lahadi.
- Kurakuran Da Wasu Ke Tafkawa A Noma Don Kasuwanci
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Asibiti, Makaranta Da Gidaje Ga Al’ummar Tudun Biri – Gwamnan Kaduna
Sanatocin sun samu tarba daga gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.
Sanata Barau, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya ce za a mika gudunmawar ne zuwa asusun gwamnatin jihar domin mika wa wadanda lamarin ya rutsa.
Gwamna Uba Sani ya mika godiyarsa ga Sanatocin da suka bayar da wannan gudunmawar.
Tawagar majalisar dattijai da suka kawo wannan jajen sun hada da shugaban kwamitocin majalisar dattawa, Sanata Micheal Opayemi Bamidele; babban mai tsawatarwa, Sanata Ali Ndume; Shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro; Mataimakin shugaban marasa rinjaye, Sanata Kamorudeen Olarere; Sanata Abdulhamid Malam-Madori; Sanata Aliyu Ikra Bilbis; Sanata Ibrahim Bomoi; Sanata Ibrahim Lamido; Sanata Abdulaziz Yar’Adua; Sanata Victor Umeh; Sanata Muntari Dandutse; Sanata Lawal Usman; da Sanata Emmanuel Udende.
Daga bisani kuma, tawagar ta ziyarci Asibitin Barau Dikko don duba wadanda suka jikkata ake kula da lafiyarsu a asibitin.