Malam Tukur Mamu wanda ke kan gaba a tattaunawar neman sakin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya karyata ikirarin sako sauran fasinjoji 27 da ke tsare a Wurin ‘yan bindigan.
A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar talata a Kaduna, Mamu ya bukaci jama’a da su yi watsi da “labaran karya” da ake yadawa dangane da sakin sauran wadanda ke tsaren.
Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara kaimi wajen ganin an sako su cikin gaggawa saboda halin da fasinjojin suke ciki na ban tausayi.
Mamu wanda shi ne mawallafin Shafin Desert Herald ya ce sauran fasinjojin da aka yi garkuwa da su na cikin wani mummunan yanayi.
A cewar Mamu, “Wannan don tabbatarwa wacce babu shakku ko kadan acikinta, cewa sauran fasinjoji 27 na jirgin kasa na hannun wadanda suka yi garkuwa da su, kusan watanni 5 da faruwar wannan lamari mara dadi.”