Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa Mazauna Kudancin Nijeriya ta yi kiran a sauya shugabannin rundunonin tsaro bisa mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai gidan gyara halinka na Kuje da kuma farmakin da aka kai wa tawagar hadiman Shugaba Buhari a kan hanyarsu ta zuwa Daura domin shirye-shiryen Babbar Sallah.
Shugaban gamayyar da ke Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Suleiman Galadanci ya ce harin na gidan gyara hakalinka da ya yi sanadiyyar ɓallewar fursunoni fiye da 600 babban bala’i ne da wasu maƙiya ƙasa ke son ganin yana aukuwa a Nijeriya.
“Lallai muna nuna takaicinmu a kan farmakin da aka kai wa tawagar shugaban ƙasa da kuma mummunan harin da aka kai gidan gyara halinka na Kuje da ya yi sanadin tserewar aƙalla fursunoni 600. Wannan al’amari ya sake caɓe yanayin rashin tsaron da ake fama da shi a arewa.
“Dan haka muna kira ga gwamnati da ta sauya shugabannin jami’an tsaro domin wannan lamarin ya kai intaha babu inda ake yi wa al’umma kisan gillah sama da Nijeriya kuma wannan abin shiryayye ne, abu ne wanda aka kasa shawo kansa. Mun daɗe muna yi wa shuganinmu bayanin cewa abubuwan da ke faruwa a arewa fa akwaifa lauje cikin naɗi, amma sun yi biris kamar ba a jikinsu ba,
“To amma idan kunne ya ji jiki ya tsira.” In ji shi.
Gamayyar matasan ta kuma ce yana daga matsalolin da suka hana shawo kan wannan rashin tsaro da ake fama, samun shugabanni nagari masu kishi, inda shugaban gamayyar ya ƙara da cewa, “A gaskiya ba mu da shugabanni nagari waɗanda za su yi kishin Nijeriya da kuma arewacin ƙasar gaba ɗaya, yanzu harin da aka kai wa tawagar shugaban ƙasa da ajali ya zo fa? Wannan babban abin kunya ne.To ya kamata mu tashi daga baccin da muke yi.”
Gamayyar matasan ta kuma yi kira ga ‘yan ƙasa nagari masu kishi su ci gaba da addu’ar Allah ya tsare gaba kar a samu makamancin irin wannan harin na Kuje da sauran ayyukan ta’addancin da ake fama da su a Nijeriya.