Harin Offa: Saraki Ya Nemi A Kara Inganta Fannin Tsaro

Daga Umar A Hunkuyi

A jiya ne,Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya yi kira da a inganta kayayyakin aikin tsaro na kasarnan, inda ya alakanta matsalar tsaron da Nijeriya ke fuskanta da rashin kayan tsaron da suka dace, ta yadda kasar ba ta iya fuskantar matsalolin na tsaro yadda ya dace.

Saraki, ya fadi hakan ne a garin Offa, ta Jihar Kwara, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Olofa na Offa, Oba Mohammed Muftau Gbadamosi, dangane da harin kwanan nan da ‘yan fashi da makami suka kai a garin.

A ranar Alhamis ne wasu bijirarrun ‘yan fashi suka kai farmaki Bankuna biyar da kuma Ofishin ‘yan sanda na garin,inda suka kashe mutane sama da 20.

“Matsalar ita ce, ta yadda za mu inganta kayan aikin Jami’an tsaron mu ne. A sarari yake, ba ma iya tunkarar duk wata matsalar tsaro yadda ya dace. Hakan ne ya sanya muka shirya wani taro kan sha’anin na tsaro akwanakin baya, domin nemo hanyar magance lamarin, mu hada kai da sashen gwamnati domin neman mafita ga matsalar tsaro na kasarnan.

“Mu a sashen Majalisa a shirye muke mu zo da shirin da ya dace da zai inganta tsaro a kasarnan, ta fuskacin samar da Jami’an tsaron da suka dace, kayan aikin su da suka shafi kudade da kuma tsari. Akwai ma maganan yin hakikanin abin da ya dace a hukumar ‘yan sanda.

“Wannan matsalar tana bukatar a tashi mata tsaye ne sosai. Matukar ba mu yi hakan ba, za mu ci gaba da gamuwa da faruwar kwatankwacin wannan abin takaicin ne, inda za a sami wasu batagari,su killace gari sukutum da guda, suna ta aiwatar da aika-aika har na tsawon awanni biyu. Ba wata al’umman da ta san ciwon kanta da za ta yi sake hakan na faruwa.”

“Muna ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su, daga fararen hula da kuma jami’an tsaro, a wannan hadarin da ya faru. A babban gari kuma cibiyan kasuwanci kamar Offa, ya zama tilas mu fuskanci matsalar tsaro yadda ya dace, don mutane su ci gaba da gudanar da ayyuikan su.”

“Tilas ne hukumar ‘yan sanda ta dauki faruwan hakan a matsayin kalubale a gare ta. Mu a namu bangaren na Majalisa, a shirye muke da mu ba su dukkanin goyon bayan da zai karfafe su,” in ji Saraki.

Kan batun ko a nemi rundunar Soji ta kasa ne da ta taimaka wa hukumar ta ‘yan sanda, Shugaban Majalisar ya ce, ba wata al’umma da ta san ciwon kanta da za ta sanya rundunan Sojin ta su rika yin aikin ‘yan sanda. Saboda hakan yana da na shi matsalar ta daban, Sojojin ma ba su da yawan da ya dace. Sannan ga shi Jihohin kasarnan su na da yawa.Wannan ya sanya yana da wuya su iya kare daukacin kan iyakokin kasarnan.”

A na shi jawabin, Oba Gbadamosi, ya sabunta kiran da wasu ke yi ne na samar da ‘yan sandan Jihohi.

“Zai fi kyau gwamnatin tarayya ta kafa rundunar ‘yan sandan Jihohi. In an yi hakan, zai sanya su fi kusanci ga jama’a, da kuma gwamnatocin Jihohin. Wannan shi ne karo na hudu da ake yi mana shigen wannan aika-aikan a cikin shekaru goma.

“Daya daga cikin matsalolin da ke guskantar hukumar ta ‘yan sanda, shi ne karancin jami’anta. Mun gano cewa, a daukacin Karamar Hukumar Offa bakidayanta, Jami’an ‘yan sandan da ke nan ba su kai hamsin ba. A duk lokacin da wani abu makamancin hakan ya ta so, ba inda muke samun wani dauki. Don haka muna fatan samun karin Jami’an ‘yan sanda. Gwamnatin Jiha za ta iya samar mana da kayan aiki, za kuma ta iya gina mana sabbin Ofisoshin ‘yan sanda, to amma ina jami’an ‘yan sandan suke, ba su da yawa.

“Kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dauki tulin daliban da suka kammala karatun su na digiri amma babu ayyukan yi, a aikin na ‘yan sanda, Sojin kasa, Sojin sama da ma Sojin ruwa. Akwai tulin matasanmu da suka gama karatun su na digiri amma ba su da aikin yi, kuma a shirye suke da su shiga ayyukan na Jami’an tsaron.”

“Sam babu tsaro a wannan kasar. Idan da a ce kana nan a ranar da abin ya faru, da ka fahimci abin da nake cewa.

“Ni ba na son na yarda da cewa, wai ba manyan makamai ne na zamani, maganan ita ce, ba za mu iya tunkarar su ba, domin ba mu da yawan da ya dace. Duk makamin da ke hannun su, Sojinmu da ‘yan sandan mu suna da su, amma in sun fi ‘yan sandan namu yawa fa,me ‘yan sandan za su iya yi.”

“Mun saba muna gayyatan agajin ‘yan banga, amma ka san wadannan ‘yan fashin sukan fadowa mutane ne ba tare da sun shirya ba. Akwai kuma hadarin amfani da ‘yan banga din, domin da zaran mun sanya su aikin, watarana kuma sai ‘yan sanda su kama su, su ce suna dauke da makamai.”

Dan Majalisar ta Dattawa mai wakiltar mazabar ta Offa da Irepodun, Sanata Rafiu Ibrahim, cewa ya yi, wannan harin da aka kai, ya nu na gazawar sashen na jami’an tsaro ne, don haka ya yi kira da a sake fasalin sashen na jami’an tsaron.

“Irin wannan abin takaicin yana iya faruwa a ko’ina, ya sanya zaman makoki a cikin garin. Zan yi kira ga Jami’an tsaron mu da su kara yawan jami’an tsaron da ke nan Offa da kewaye. Hakan kuma ya nu na cewa, muna da bukatar a kafa mana barikin Soji a nan Offa da kewaye, da za su iya taimakawa ‘yan sanda a irin wannan lokacin,” in ji Ibrahim.

 

Exit mobile version