Abba Ibrahim Wada" />

Harry Kane Zaiyi Jiyyar Makwanni – Mourinho

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harry Kane zai shafe makwanni yana jinyar raunukan da ya samu a idanun sawayensa, yayin fafatawar da suka sha kaye a hannun Liberpool da 3-1 a ranar Alhamis.
Kane ya samu rauni na farko ne a idon sawunsa na dama bayan taho mu gamar da suka yi da dan wasan tsakiyar Liberpool Thiago Alcantara, ya yin da kuma ya samu rauni na biyu a idon sawunsa na hagu, bayan karafkiyar da Jordan Henderson.
Tun bayan tashi daga wasan dai kociyan kungiyar ya bayyana cewa dan wasan nasa ya samu ciwo kuma yana ganin zai shafe makonni ba tare daya bugawa kungiyar wasa ba har sai likitocin kungiyar sun bashi damar fara wasa.
A kakar wasa ta 2017 da 2018 Harry Kane ya taba samun irin wannan rauni da ya shafe makwanni 6 yana jinya kafin murmurewa wanda hakan yasa kungiyar ta rage kokari fiya da lokacin da yake buga wasa.
A shekarar 2016 ma dan wasan ya yi jinyar tsawon akalla makwanni 4, saboda raunin da ya samu a idon sawun nasa sai dai tafiyar dan wasa Kane a kungiyar Tottenham ba karamar barazana yake zama ba musamman ga sakamakon wasannin kungiyar.

Exit mobile version