Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar Alhaji Faruq Umar, kwamishinan Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata ta Tarayya mai wakiltar shiyyar Arewa Maso Gabas.
Marigayin ya yi hatsarin ne da sanyin safiyar Lahadi a kan babbar hanyar Jakusko zuwa Gashu’a yayin da yake dawowa bayan ziyarar jaje da ya kai garin Jakusko.
- PSG Na Duba Yiwuwar Sayar Da Mbappe Kafin Kwantiraginsa Ya Kare
- An Ceto Mutum 3 Bayan Musayar Wuta Da ‘Yan Bindiga A Jihar Kwara
Mataimakin gwamnan Jihar Yobe, Idi Barde Gubana na daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka halarci sallar jana’izar marigayin.
Addu’ar karkashin jagorancin tsohon mai bai wa gwamna Buni shawara kan harkokin Addini, Ustaz Babagana Mallam Kyari, an gudanar da addu’ar a garin Gashu’a, hedikwatar karamar hukumar Bade ta jihar.
Bayan haka mataimakin gwamna Gubana ya jajanta wa iyalan mamacin da kuma al’ummar karamar hukumar Bade bisa wannan babban rashi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya bukaci iyalinsa su kasance masu yi masa addu’a.
Faruq Umar ya rasu yana da shekara 52 a duniya, ya bar mata biyu da ‘ya’ya shida.