Bankin Duniya ya bayyana cewar hauhawar farashin kayayyaki ya sake jefa ‘yan Nijeriya miliyan 10 cikin kangin talauci.
Wannan na cikin wani rahoton shekarar 2023 da bankin ya fitar, inda ya ce samun kudin shiga a kasar bai yi daidai da hauhawar farashin kayayyaki ba, wanda hakan ya jefa mutanen kasar da dama cikin talauci.
- Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara
- Tarihin Masarautar Zazzau Da Sarakunansu (5)
Kididdigar ta yi gargadi kan yadda talauci ke kara yawa a kasar, inda ya kai kashi 30.9 cikin dari na al’ummar da ke rayuwa a kasa da dalar Amurka $2.15 a kowace rana.
Abubuwan da suka yi wa kasar tasiri sun hada da dogaro da danyen mai, rashin samar da kudaden shiga, hauhawar farashin kayayyaki da sauran kalubalen tattalin arziki, wadanda na daga cikin abubuwan da suka dagula al’amura a Nijeriya.
Duk da tsare-tsaren da shugaba Bola Tinubu ya fito da su, na habaka tattalin arziki, saka hannun jari daga kasashen waje, da rage talauci, amma talauci na kara yawa a kasar.
Ministan Kudi, Wale Edun, a wata ziyara da ya kai birnin Washington, ya bayyana yakinin cewar tattalin arzikin kasar zai habaka nan ba da jimawa ba.
A cewarsa hakan zai rage hauhawar farashin kayayyaki da aka samu a kasar, wanda zai kai ga rage kangin talauci da wasu al’ummar kasar ke ciki.