Duniya ta dau dimi dangane da hari na farko da Kasar Iran ta kai wa Isra’ila a matsayin ramuwar gayya bayan Iran ta zargi kasar ta Yahudu da kai harin bama-bbamai da ya kashe mata manyan janar na soja da wasu kananan dakaru a ofishin jakadancinta da ke Siriya.
Hankulan kasashe sun karkata ga yadda za a shawo kan rikicin da ke neman barkewa tsakanin Iran da Isara’ila wanda ake ganin zai kara tagayyara halin da yankin gabasa ta tasakiya yake ciki na tashe-tashen hankula.
- Sauyin Yanayi: Dabarun Da Za Su Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi
- Wani Mutum Ya Mutu Bayan Ya Cinna Wa Kansa Wuta A Yayin Da Ake Shari’ar Trump
Rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta kai harin ne a ranar Asabar da dare tare da jirage marasa matuka da makamai masu linzami akalla 300 wanda Isra’ilar ta yi ikirarin cewa ta samu nasarar tarwatsa kusa kashi 90 na adadinsu kafin su kai ga fadawa kasarta bisa amfani da na’urorin tsaron sararin samaniya bisa goyon bayan Amurka da Birtaniya.
Amma kuma Babban Hafsan Sojojin Iran, Manjo Janar Abdolrahim Mousabi ya ce harin na Iran ya samu gagarumar nasarar da ake bukata, kana ya ce ba za su ci gaba da kai sabbin hare-hare ba amma da Zarar Isra’ila ta yi gangancin cewa za ta rama, to kilu za ta jawo bau.
Harin da Iran ta kai wa Isra’ila ya haifar da zaman dar-dar a yanking abas ta tsakiya fiye da yadda aka gani tun farkon fara yakin Isra’ila da Hamas a watan Oktoba, yayin da Washington ke neman daukar matakan diflomasiyya domin sassauta rikicin yankin.
An bayar da rahoton cewa, wata yarinya kawai ta samu rauni a Kudancin Isra’ila, sannan kuma makami mai linzami ya afka wa wani a sansanin sojin Isra’ila, wanda bai yi wata barna ta a zo a gani ba.
Mona Yacoubian, Mataimakiyar Shugabar Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Amurka A Yankin Gabas da Arewacin Afirka USIP, ta ce Iran ta yi nasarar mayar da martani a game da harin da aka kai Damascus.
“Dukkansu (Iran da Isra’ila) a wannan lokacin na iya yin ikirarin nasara, sannan kuma za su iya sauka daga dokin zuciyar da suke kai, musamman domin ganin an ceto fararen hular Isra’ila.”
Masu tsattsauran ra’ayi na Isra’ila sun matsa kaimi kan mayar da martani, amma wasu sun ba da shawarar kamewa, suna masu cewa kamata ya yi Isra’ila ta mai da hankali kan karfafa cudanya da abokan huldarta na Larabawa.
“Za mu kafa rundunar hadin gwiwa a yankin domin mayar da martini ga Iran a lokacin da ya dace da mu,” in ji Benny Gantz, mamba na Majalisar Dinkin Duniya.
Manazarta sun ce Iran ta aike da sakon cewa za ta kara sauya ka’idojinta na yaki da Isra’ila matukar ta ce za ta mayar da martani.
Magnus Ranstorp, Mai Ba Da shawara Kan Dabaru a Jami’ar Nazarin Tsaro ta Sweden ya ce “Harbin wadannan makamai na Iran gargadi ne, yana ami cewa idan kuma Isra’ila ta kuskura ta karya doka, to fa sakamakon da zai biyo baya ba mai kyau ba ne.”
Sai dai Iran ta ce ba ta neman barkewar yaki a yankin. Ministan Harkokin Wajen Kasar Hossein Amirabdollahian ya fada cikin wani sakon da ya wallafa a shafin D, ko kuma Tuwita, cewa Iran ba ta da niyyar ci gaba da gudanar da wannan aiki na kare kanta a wannan lokaci sai dai idan an kai mata hari.
Iran ta jaddada cewa ta kai hari kan cibiyoyin Isra’ila da ke da hannu a harin Damascus, ba a kan farar hula ko “yankunan tattalin arziki ba.”
Bayan da Isra’ila ta fara kai hare-hare a Gaza kan Hamas, kungiyoyin da Iran ke mara wa baya sun yakin. Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba rokoki zuwa Arewacin Isra’ila. ‘Yan tawayen Houthi na Yamen sun kai hari kan jiragen ruwa na Yammacin Turai a Tekun Bahar Maliya.
Wata tawagar mayakan sa kai na Iraki da ke samun goyon bayan Iran ta kai hari kan sansanonin sojojin Amurka a Iraki da Siriya.
Da alama Isra’ila ta hakura da daukar matakin soji domin ba ta da goyon bayan haka a tsakanin kawayenta ciki har da Amurka, in ji Eldad Shabit, wanda ke jagorantar shirin Bincike na Cibiyar Fasahar Isra’ila A Kan Tsaro ta Kasa.
Kakakin fadar White House John Kirby ya shaida wa NBC cewa Shugaba Joe Biden ba ya kaunar ganin tabarbarewar tsaro a yankin ko kuma “yaki mai tsanani” da Iran, kuma hakan ya nuna yana “aiki a bangaren diflomasiyya da kansa.”
An gudanar da tarukan gaggawa na G7 – taron kasashe masu ci gaban masana’antu da suka hada da Amurka, Birtaniya, da Faransa – da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Mahalarta taron na G7 a cikin wata sanarwa da suka fitar sun yi tir da harin na Iran, suna masu cewa “a shirye muke mu dauki karin matakai a yanzu da kuma mayar da martani ga ci gaba da shirye-shiryen hargitsa zaman lafiya.”
Wasu masu alaka da Kungiyar Marubuta ‘Yan Jarida Josef Federman a Urushalima, Abby Sewell a Beirut, Amir Bahdat a Tehran da Thomas Adamson a Paris sun ba da gudummawa ga wannan rahoton.
Amurka Ta Kwaye Wa Isra’ila Baya
A yayin da Isra’ila ke nazarin yadda za ta mayar da martani kan harin da Iran ta kai mata a karshen mako, Amurka ta kwaye mata baya yayin da ta bayyana cewa babu ruwanta idan har kasar ta zabi daukar fansa ta hanyar soji.
Sakon na Amurka da ba a saba ganin irinsa kan babbar aminiyarta da ta ke bai wa taimakon soji fiye da kowace kasa a duniya, ta ce ba za ta shiga rikicin Iran da kuma Isra’ila ba.
Bayan watanni da Isra’ila ta yi na daukar fansa a Gaza, duk da suka daga Amurka da sauran kawayenta da ke cewa ayyukan sojinta sun wuce gona da iri.
Gwamnatin Biden ta bayyana karara cewa, tana tsoron yaki mafi girma ya barke a Gabas ta Tsakiya.
“Mun yi imanin Isra’ila na da ‘yancin daukar mataki don kare kanta, amma wannan wani salo ne na siyasa,” in ji wani babban jami’in fadar White House ga manema labarai jim kadan bayan kawo karshen harin na Iran. ”
Da wani dan jarida ya tambaye shi ko Amurka za ta taimaka wa Isra’ila wajen tunkarar hare-haren soji, nan take ya ce a’a.
Amurka ta ce tuni ta isar da wannan sakon kai tsaye ga manyan jami’an Isra’ila a wata ganawar sirri ta wayar tarho da ta gudana tsakanin sakataren tsaro Lloyd Austin da ministan tsaron Isra’ila Yoab Gallant.
Harin da Iran ta kai kan Isra’ila da yammacin ranar Asabar ya sha kakkausar suka daga shugabannin duniya, ciki har da jami’an Amurka wadanda da farko suka yi tunanin kasar ta yi amfani da makamai masu linzami guda 12.
Harin dai, Iran ta kira shi a matsayin ramuwar gayya bayan harin da Isra’ila ta kai ofishin jakadancinta da ke Damascus na Kasar Syria.
Kasar Sin Ta Yi Tir Da Harin Ofishin Jakadancin Iran A Siriya
Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian sun tattauna ta wayar tarho a ranar 16 ga watan Afrilu dangane da takun saka tsakanin Isra’ila da Iran.
Sashen Hausa na CGTN, ya ruwaito cewa, Amir-Abdollahian ya bayyana wa Wang matsayin Iran kan harin da aka kai a sashin karamin ofishin jakadancin Iran a Birnin Damascus na Kasar Syria. Yana mai cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bai bayar da martanin da ya dace kan wannan harin ba, kuma Iran na da hakkin kare kanta, a matsayin mayar da martani ga take hakkinta.
Amir-Abdollahian ya ce, halin da yankin ke ciki a halin yanzu yana da matukar muhimmanci, kuma Iran a shirye take ta kai zuciya nesa, kuma ba ta da niyyar kara ta’azzara lamarin.
A nasa bangaren kuwa, Wang ya ce, kasar Sin na matukar yin Allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kai kan sashin karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, tare da mai da shi a matsayin babban cin zarafin dokokin kasa da kasa, kuma ba za a amince da hakan ba.
Kasar Sin ta lura da furucin na Iran na cewa matakin da ta dauka yana da iyaka, kuma wani mataki ne na kariyar kai a matsayin martani ga harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran a Syria, a cewar Wang.
Ya kara da cewa, an yi imanin cewa Iran za ta iya tafiyar da lamarin yadda ya kamata, tare da kiyaye zaman lafiya a yankin da kare ikonta da martabarta.
A wannan rana, Wang Yi ya kuma tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud, game da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma alakar Sin da Saudiyya.
Ra’ayoyin Kasashen Duniya
Duniya ta kira taron gaggawa domin nazari a kan hare-haren da Iran ta kai wa Isra’ila na ramuwar gayya, yayin da kasashen duniya ke bayyana damuwa dangane da barazanar barkewar yaki a tsakanin kasashen biyu.
Sakatare Janar na majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana damuwa dangane da barazanar tabarbarewar al’amura a yankin gabas ta tsakiya.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana matukar damuwa game da tabarbarewar yanayin da ake ciki , ta kuma yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankula domin kauce wa sake ta’azzara yanayin zaman dar-dar da ake ciki.
Ma’aikatar ta ce kara tabarbarewar lamura, alama ce ta mummunan tasirin rikicin Gaza na baya-bayan nan, don haka abu mafi muhimmaci a yanzu shi ne maida kai wajen aiwatar da kudurin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2728, da gaggauta kawo karshen rikicin Gaza.
A daya bangaren kuma, Sin ta yi kira ga sassan kasa da kasa, musamman kasashen da ka iya yin tasiri a lamarin, da su taka kyakkyawar rawa wajen kare zaman lafiya da daidaito a yankin.
Shugabar gudanarwar kungiyar kasashen Turai, Ursula bon der Leyen ta bukaci Iran da ta gaggauta tsagaita wuta da kuma kiran kasashen da su tsagaita wuta tare da aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya.
Sakatare Janar na kungiyar kawancen tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce sun yi Allah-wadai da abin da ya kira matakin na Iran, yayin da suke ci gaba da sanya ido a kan abin da ke faruwa.
Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak da takwaransa na Canada Justin Trudeau duk sun bayyana harin na Iran a matsayin na rashin hankali inda suka sake jaddada goyan bayansu ga Isra’ila.
Ita kuwa Rasha da Saudiyya duk sun yi kira ne a kai zuciya nesa tare taka-tsan-tsan, kamar yadda ita ma Katar ta bukaci manyan kasashen duniya su dauki matakin kwantar da hankalin bangarorin.
Sakamakon rashin samun goyon bayan Amurka kan mayar wa Iran martanin soji, a halin yanzu wasu na ganin Isra’ila ta shiga tsaka mai wuya saboda shugabanninta na samun matsin lamba a cikin gida na dawo da wadanda Hamas take garkuwa da su sannan ga zafin rashin samun goyon bayan daukar matakin soji a kan Iran kana ga tabarbarewar alaka a tsakaninta da wasu kasashen Larabawa masu makwabtaka da ita.