Hawan Nassarawa na daya daga cikin bikin hawan Sallah da sarkin Kano ke yi duk shekara, inda yake kai ziyara gidan gwamnatin Kano don ganawa tare tattauna matsalolin mutane ga gwamnan jihar.
Sai dai a wannan karon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, a karon farko tun bayan hawansa karagar mulki a ranar 9 ga Maris 2020 ba zai ziyarci gidan gwamnatin jihar Kano ba.
- Yadda ‘Yan Uwa Suka Biya Miliyan 800 Don Sakin Fasinjoji Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
- Zabar Mataimaki: Tinubu Ya Watsa Wa Gwamnonin Arewa Maso Yamma Kasa A Ido
Wata majiya mai tushe ta sanar da LEADERSHIP cewa dalilin da yasa sarkin ba zai ziyarci gidan gwamnatin ba shi ne Ganduje ba ya gari.
Majiyar ta ce gwamnan ya je Abuja yayin da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna, ya tafi kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji.
Sarkin Kano Muhammad Abbas ne ya kirkiro Hawan Nassarawa na Gargajiya a shekarar 1906 inda ya ziyarci Kano wanda ya yi mulkin mallaka bayan kwana biyu da Sallah domin yin mubaya’a.
Sarakunan da suka gaje shi daga 1906 zuwa yanzu, sun ci gaba da kasancewa akan al’adar duk da cewa turawan mulkin mallaka sun mika ‘yanci ga ‘yan Nijeriya.