Daga Husseini Yero,
A ranar Alhamis, Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ya soke zoyarar da ya yi zuwansa Jihar Zamfara, domin yin jaje kan abubuwan da suka faru ga al’ummar wannan jiha na kisan da ‘yan bindaga suke musu.
An sa ran cewa Shugaba Buhari bayan kammala ziyarar bude ayyukan kamfanin Simintin BUA da na sashen lantarki a Jihar Sakkwato, zai garzaya Jihar Zamfara.
Bayani janye wannan ziyara ta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Zamfara, Honarabul Bello Muhammad a lokacin da yake yi wa masu taryar shugaban kasa a fadar gidan gwamnatin jihar da ke Gusau bayani a kan musabbabin rashin zuwan shugaban.
Haka kuma, ya kara da cewa, soke wannan ziyarar ya biyo bayan yanayin da aka wayi gari da shi ne hazo, wanda kuma wannan yanayin ba zai bayar da daman tashin jirgin sama ba.
Gwamna Matawalle ya kuma bayyana cewa, za a sake sa wani lokaci nan ba da dadewa ba, wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buharin zai kawo musu ziyara ta musamman.