Hedikwatar tsaro ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su bayar da bayanan kan wasu ‘yan ta’adda 97 da ake nema ruwa a jallo, wadanda ke haddasa munanan laifuka a kasa.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba ne ya tabbatar da sunaye da hotunan mutanen da aka bayyana ana nema ruwa a jallo a ranar Juma’a.
- Matsalar Tsaro A Nijeriya: Akwai Bukatar Daukar Kwakkwaran Mataki
- Tsaron Iyakoki: ACG James Sunday Ya Jagoranci Taron Samar Da Dabarun Aiki A Jos
Idan dai za a iya tunawa, a watan Nuwamban 2022 ne sojoji suka bayyana cewa za a gurfanar da shugabannin ‘yan bindiga 19 tare da bayar da ladan naira miliyan 5 ga duk wanda ya fallasa ‘yan ta’adda don a karfafa guiwar ‘yan Nijeriya su bayar da bayanan yadda za a kai ga kama masu laifin.
Sai dai kuma a wannan lokacin ba a bayar da wata kyauta kan bayar da bayanai kan mutane 97 da aka bayyana ana nema ruwa a jallo ba, wadanda suka hada da shugaban kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biafra, IPOB.
Sunaye da hotunan sun kunshi ‘yan ta’adda daga Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma masu tayar da kayar baya a Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.
Kimanin mutane 43 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a shiyyar Arewa maso Yamma, daga cikinsu akwai Alhaji Shingi da Malindi Yakubu Boka da Dogo Gide da Halilu Sububu da Ado Aliero da Bello Turji da Dan Bokkolo da Labi Yadi da Nagala da Saidu Idris da Kachalla da Rugga da kuma Sani Gurgu.
Kazalika, an bayyana mutane 33 da ake nema ruwa a jallo a yankin Arewa maso Gabas sakamakon rikicin Boko Haram da kungiyar IS mai da’awar kafa daular musulunci a yammacin Afirka.
Wasu daga cikin ‘yan ta’addar da ake nema ruwa a jallo sun hada da Abu Zaida da Modu Sulum da Baba Data da Ahmad da Sani Teacher da Baa Sadiq da Abdul Saad da Kaka Abi da Mohammad Khalifa da Umar Tella da Abu Mutahid da Malam Mohammad da kuma Malam Tahiru Baga da kuma Uzaiya da Ali Ngule.
A halin da ake ciki dai an bayyana cewa ana zargin masu tada kayar baya 21 da kuma masu aikata laifuka a yankin Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.
Wadanda ake tuhuma da laifin sun hada da Simon EkpaEkpa da Chika Edoziem da Egede da Zuma da ThankGod da Gentle da Flavour da Mathew da David Ndubuisi da High Chief Williams Agbor da Ebuka Nwaka da Friday Ojimka da Obiemesi Chukwudi aka Dan Chuk da David Ezekwem Chidiebube da Amobi Chinonso Okafor mai inkiyar Temple da dau sauransu.