Tsohon ɗan wasan Arsenal da Faransa Thierry Henry na ɗaya daga cikin sunayen da ake tunanin zai maye gurbin Rob Page a matsayin kocin tawagar ƙwallon kafa ta ƙasar Wales.
Henry, wanda ya jagoranci Monaco da Montreal Impact, shi ne ke jagorantar tawagar ‘yan ƙasa da shekara 21 na ƙasar Faransa kuma yana shirin jagorantar tawagar masu masaukin baki a gasar Olympics da za a yi a birnin Paris a wata mai zuwa.
- Gasar Euro 2024: Yadda Kasashe Suka Gayyaci ‘Yan Wasa
- Kayayyakin Wasanni Kirar Kasar Sin Sun Samu Yabo A Gasar Wasannin Afirka Ta 13
Tsohon ɗan wasan mai shekaru 46 yana da alaƙa da Wales, bayan da ya yi karatu a hukumar kwallon ƙafa ta Wales (FAW), hukumar ta FAW ta kori Page a ranar Juma’ar da ta gabata bayan shafe shekaru uku da rabi yana jan ragamar kungiyar sakamakon gazawar Wales wajen samun tikitin shiga gasar Euro 2024.
Hukumar ba za ta ɓata lokaci wajen naɗa wanda zai gaji Page ba, inda take fatan ganin tayi hakan kafin wasan da za ta buga a gida da Turkiyya a watan Satumba.