Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta musanta zargin da ake yi wa jami’anta na cin zarafin wata budurwa mai suna Hauwa’u Lawal, wanda ya kai ga karya mata kafa kamar yadda wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ke bayyanawa.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Lahadi a Katsina, Mataimakin Kwamandan Ayyuka na Hukumar, Malam Mohammad Shu’aibu, ya bayyana ikirarin a matsayin karya da sauya gaskiyar lamari.
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja
- Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
A cikin faifan bidiyon da aka yada, Hauwa ta yi zargin cewa, jami’an Hisbah sun yi mata dukan tsiya a lokacin da ta ziyarci dan uwanta da ke tsare a hannunsu.
Ta ce, sakamakon dukan da ta sha, ta samu karaya a kafa da kuma raunin da ya shafi kunnenta.
Sai dai Shu’aibu ya musanta wannan ikirarin, inda ya tabbatar da cewa, an kama dan uwanta ne a yayin wani samame da aka gudanar a wurin wani shagali a birnin Katsina.
A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne da laifin yin sojan gona da kuma yunkurin dakatar da jami’an Hisbah a lokacin da suke bakin aiki.
Da yake karin haske game da gaskiyar lamarin abinda ya faru, Shuaibu ya ce, an hana Hauwa shiga cikin ofishin Hisbah ne saboda irin tufafin da take sanye da su na rashin da’a, kuma ta yi yunkurin marin daya daga cikin jami’an Hisbah a lokacin da suka hana ta shiga.
Dangane da ikirarin da Hauwa ta yi na karaya a kafa, Shu’aibu ya ce hukumar ta bukaci iyalanta da su kawo mata shaidar na’urar haska kashi amma har zuwa lokacin taron manema labarai ba su samu wani takarda da ke tabbatar da raunin da ta samu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp