Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe, ta lalata katan 51 na giya a wani yunƙuri na inganta tarbiyya da tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.
An gudanar da aikin lalata giyar a Damaturu, babban birnin jihar, inda jami’an hukumar da wasu suka shaida lamarin.
- Har Yanzu Shugabanci NNPP Na Hannunmu – Tsagin Kwankwaso
- An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
An kama giyar ne a lokuta daban-daban na samamen da hukumar ta Hisbah ta kai a sassa daban-daban na jihar.
Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe, Dr. Yahuza Abubakar, ya ce wannan mataki ya yi daidai da dokokin jihar da suka haramta sayarwa da shan giya.
Ya bayyana cewa manufar aikin shi ne tabbatar da tarbiyya da kyawawan ɗabi’un al’umma.
Ya ce shan giya yana barazana ga lafiyar jama’a tare da haddasa matsalolin zamantakewa.
A cewarsa, hana yaɗuwar giya zai rage aikata laifuka da kuma inganta zaman lafiya.
Dr. Yahuza ya kuma buƙaci al’umma da su mara wa Hisbah baya ta hanyar bayar da rahoto kan duk wani abu da ke saɓa wa doka.
Ya tabbatar da cewa hukumar ta ƙudiri aniyar ci gaba da aiki don tabbatar da adalci, zaman lafiya da gyara halayyar al’umma a Jihar Yobe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp