ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Yanzu Shugabanci NNPP Na Hannunmu – Tsagin Kwankwaso

by Yusuf Shuaibu
1 year ago
Kwankwaso

Jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Dakta Ajuji Ahmed mai biyayya ga Dakta Rabiu Musa Kwankwaso sun bayyana cewa yar yanzu shugabancin NNPP na hannunsu duk da hukuncin da kotu ta yanke a baya-bayan nan dangane da rikicin shugabancin da ake fama da shi a jam’iyyar.

Tun bayan zaben 2023, jam’iyyar NNPP ta shiga cikin rudani kan shugabanci, inda bangarorin da ke hamayya da juna ke fafatawa kan yadda za su tafiyar da shugabancin jam’iyyar, alamomi da tsarin NNPP.

  • Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
  • UBEC Ta Yaba Wa Jigawa Kan Inganta Harkar Ilimi A Jihar

Rikicin dai ya haifar da ruDani a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da magoya baya, musamman a Kano, inda a halin yanzu jam’iyyar NNPP ke rike da madafun iko a jihar.

ADVERTISEMENT

Wata babbar kotu da ke da zama a Abuja ta yi watsi da karar da tsagin Kwankwaso ya shigar. Kotun ta kalubalanci sahihancin wani bangare karkashin jagorancin Dakta Boniface Aniebonam da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Agbo Major, wanda shi ma ya yi ikirarin shi ne halastaccen shugabancin jam’iyyar.

Shari’ar da Dakta Ajuji Ahmed da wasu mutum 20 suka shigar, ta nemi a soke ikon kwamitin amintattu na NNPP da bangaren zartarwa da suka hada da sakataren jam’iyyar na kasa na daya bangaranci, Oginni Olaposi, mataimakin shugaban jam’iyyar, Cif Felid Chukwurah da kuma lauya, Tony Obioha.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP.

Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar.

Kwankwaso
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Spaniya

Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Spaniya

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.