Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta koka kan nuna halin rashin kula da Iyaye ke yi ga yaransu a jihar bayan ta ceto yara 230 da ke zaune a kan titunan Kano.
A cewar babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, an gano yaran ne a wani samame da aka kai a wuraren haɗuwar jama’a kamar kasuwanni da wuraren ajiye motoci.
- Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
- Ma’aikatar Wajen Sin: Yamadidin Da Ake Yi Na “An Tilasta Wa Mutane Yin Aikin Dole” Karya Ne
Aikin ceton yaran, ya bayyana a fili irin rayuwar kunci da yaran ke ciki, inda aka samu gawarwakin yara hudu a wajen saboda yanayin sanyi, wasu kuma na fama da matsananciyar rashin lafiya.
Daurawa ya jaddada bukatar a gaggauta samar da mafita mai dorewa don magance wannan matsalar da kuma nusantar da iyaye illar barin ‘ya’yansu barkatai ba tare da lura da su ba. Inda ya nuna hakan kan janyo a yi amfani da yaran wajen aikata laifukan da basu kamata ba.