Hakika Nijeriya kasa ce da ta ke bukatar jagoranci nagari kuma abin koyi, duba da yadda aka sha wahala daban-daban ga rashin zaman lafiya ga talauci da rashin ayyukan yi da sace-sacen mutane a yanzu, wanda ya yi katutu ga matsalar karancin ababen more rayuwa ga shi kullum matsala yau matsala gobe, ga rashin imani na wasu shugabanni da su ke wawashe dukiyar kasarnan daga su sai yayansu, kasa ta zama sai dai kaji abu a baki ko a rubuce, amma babu aiwatar wa kamar yadda ya kamata, kwana kwanannan akayi kididdiga da shugaban yaki da cin hanci da rashawa na kasa yayi, yace daga 2011-2015 anyi asarar Naira kimanin Tiriliyan Daya da Biliyan Uku a tsakanin mutane da basufi mutum talatin ba da kamfaninnika uku ba, wanda a kalla za’a iya samar da hanyoyi masu tsawon kilomita dari biyar da kuma inganta ilmin yara tun daga firamari zuwa su gama jami’a har su dubu hudu, wanda kowanne zai iya samun miliyan 24.
Sannan wani hasashe daya fito kwana kwanannan a duniya gaba daya Najeriya itace kasa ta shidda a jerin kasashen da alumarta suke fama da kuncin rayuwa, saboda haka wannan babban kalubale ne da yake gaban shugaba Muhammad Buhari da gwamnonin jihohi da yan majalisar dattawa data wakilai dama sauran yan majalisa na jihohi, saboda haka yakin bana shugaban kasa bane kadai harda wadanda na lissafa a sama kuma wani abin takaici kwana-kwanannan wata kungiya mai zaman kanta ta fitar da wani rahoto da yake nuna cewar babu inda cin hanci yafi katutu a yanzu a kasar nan irin sashen yan sanda da kotunan shari’a da ma’aikatun ilmi dana lafiya, lallai biri yayi kama da mutum domin irin abubuwa da suke faruwa na aikata laifika kullum sai tufka akeyi amma ana warwarewa, ga laifuka kullum sai dada faruwa su ke yi amma an kasa gyarawa, kullum kuma makudan kudade ake narkawa amma babu wani cigaban azo a gani, sannan ita kanta ma’aikatar shari’a, duk da suna da tsarin albashi maikyau.
Amma ga shari’o’i nan a jibge sai wasa ake da hankulan jam’a, mai galihu duk kazantar laifinsa daya dauki lauya sai yakai labari, amma marasa galihu na nan a kurkuku ba a sa ranar da za’a kaishi katu ba, wani laifinsa baifi matsalar dubu uku ba, amma ga wanda yayi ta’adin biliyoyun nairori yana shaker iskar yanci, saboda yana da kudi lallai shugaba Buhari wannan karon yana da jan aiki, ya kuma san su wanene abokan aiki na kwarai kada yayi la’akari da abokai ko asali ko daukaka ko tarin ilmi amma ba inganci aa ya duba nagarta da aiki tukuru da kishin kasa wajen zabo abokan aiki. Kuma rike shugabancin a kasarnan a halin yanzu sai mutum yayi da gaske, sauda yawa zaka tarar da mutumin kirki mai amana, amma ana bashi dama sai kaga ya canja ya koma wani azzalumi.
Ka ga a nan kadai alumma ne suke zuga mutum ko a iyalansa suyi ta kawo masa wasu bukatu da zai kauce hanya ko yan uwa da abokai duk wadannan dana lissafa sune kanwa uwar gami wajen sa mutum ya kauce hanya ya zama mahan dami in ya sami mukami, waje daya wasu iyaye suna da rawar takawa wajen banbance da mai shi da marashi, domin wanda bashi dashi bama a sashi a layin wata shawara, amma maishi koda dan auta ne shine da nagari tamkar da goma, to kaga nan ma akwai matsala. Sannan wasu malamai da matsafa na taimakawa ayi zalunci domin a biya su, sai kaga mutum yayi cuta, amma maganar ta mutu, ko mutum ya samu damar da zaiyi ya cuta a wani matsayi amma yaki tafiya, saboda anayi masa rokon Allah ko anayi masa tsafe-tsafe.
Sannan su kansu alumma kaso 95 cikin 100, kallo ya koma sama, misali wanene yake da mota ta gani ta fada, wanene yake da gida nagani na fada, wanene yafi kowa shiga mai tsada, ko tara dukiya ko samun wani matsayi babba to nan ido yana kai a shiga zan tuttuka a gari sai a shiga kwadayi da tumasanci ko neman gindin zama, wannan tasa koda mutum ya samu kansa a abubuwan dana lissafa zai fara gudun mutane ko kasha waya, lallai mutane ya kamata a rage irin wannan zalama a wurin wasu madaukaka, kai yau ko mutuwa akayi ido yana kan wanda yazo da wata shiga mai kyau, ko wani matsayi, lallai alumma suma suna da nasu laifin, domin kamannin shugabannin mu kamannin talakawan kasa, a gyara kowa yaci gaba da harkokinsa, ya kuma tsaya a matsayin da Allah ya bashi, a kuma hakura da dan abin da Allah ya hore masa, ba kwadayin abin mutane wanda shi yake haifar da nuna munafunce-munfunce da gaba ko zagin muatane, inda haka zata faru su kansu masu halin ne zasu rika neman talakawa ganin basu damu da abin hannunsu ba. Amma zamani ne yazo babu abin da yafi kudi da ado tasiri, saboda haka lallai shugaba Buhari indai zai magance matsalolin kasarnan tun daga tushe to sai yayi wani tsari da yaki da irin wadannan matsaloli domin sune suka hana ruwa gudu ko kuma suke haddasa kwam-gaba kwam-baya, a kasa samun cigaban daya dace.
Sannan lallai sashen ilmi da lafiya a ko’ina sai anyi da gaske domin sanin su wanene jagororin wadannan sassa? Me suke ciki, a nan ya kamata ayi wannan babban garambawul domin babu yadda za’ace akwai cigaba kaga mutum yar rashin lafiya bata kai ta kawo ba ace za’a fita waje neman magani, ina asibitocin mu? Kuma wato talaka ne kawai zai zauna cuta ta kasha shi ko tana kassara shi? Lallai a gyara wannan tsarin haka, bangaren ilmi ba gwaninta bace ba kuma burgewa bace ace a kwashe kudi makudai ana biyawa wasu tsirari kudade suna zuwa karo karatu kasashen waje, ina makarantun yayan talakawa? makarantunsu a lalace wata kididdiga da akayi ta nuna duk yaro da ake biyawa karatu domin yaje yayi digirin farko a kasar waje shekaru3 ko 4, ana kasha masa kusan naira miliyan goma sha biyar in akayi hakan sau dubu biyu zai iya gyara makarantun firamare dana sakandare dubu goma na yayan talakawa a samarmusu da wadatattun ababan koyarwa da isassun korarrun malamai, saboda haka a sake tunani.
A nan a na wata ga wata, a na maganar jita-jita wai za’a kara kudin man fetur saboda dillalan man fetur suna bin gwamnatin tarayya naira biliyan dari takwas, to abin tambaya ta ina wannan bashi ya samu? Sannan wasu suna has ashen cewar wai shugaba Buhari baya shirya taruka da gwamnonin arewa, karfa a manta shugaba Buhari na alummar najeriya ne bawai na arewa kadai ba, ina tarin kudaden da ake bawa gwamnonin arewacin kasarnan kashi-kashi? Ina maganar kungiyar gwamnoni na arewa? Yanzu duk wadannan bai isa su inganta arewacin kasarnan ba sai ana taiwa shugaban kasa surutu.
Sannan abin tambaya wadannan arin ayyuka ne da ake bukata shugaban kasa ya sa hankalinsa akai? Sannan wane irin ayyuka shugaban kasa ya yi a kasa da arewacin kasarnan? A takaice dai arewacin kasarnan ina ya dosa a tara a sati mai zuwa domin jin sabon wannan babi. Lallai ko anaso ko anaki sai an dawo da bunkasa kananan hukumomi da ababan more rayuwa, ma’ana kudaden da ake kashewa a sama to adawo da kashesu a matakan kasa wannan shi zai tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki a kasarnan baki daya, saboda haka munasan ran kasafin kudin bana na 2019 zai tafi da kaso 70% wajen inganta rayuwar karkara da ababan more rayuwa da kawar da matsalar tsaro tun daga tushe.
A biyo ni bashin wannan magana.
Yakasai ya rubuto ne daga Kano. Za a iya samun sa a lambar waya 08054407095 ko imel abidyk62@gmail.com
Jami’ar Tarayya Ta Gusau Ta Musanta Labarin Harin ‘Yan Bindiga
Daga Hussaini Yero, Shugabannin Jami'ar gwamnatin Tarayya dake Gusau (FUG)...