A ranar 13 zuwa 20 na watan Nuwamban 2022 aka gabatar da shirin bayar da kiwon lafiya kyauta karo na 7 wanda da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, Hon Mohammed Garba Datti Babawo yake daukar nauyi a Asibitin Railway da ke karamar hukumar Sabon Gari.
Mataimakin Editanmu Bello Hamza ya duba tasirin shirin da yadda al’umma suka amfana a tsawon lokacin da ke gabatar da shirin. Ana gudanar da shirin ne a karkashin jagorancin kwararren Likitan nan mai suna Dakta Joshep Haruna Kibu wanda yana daga cikin shugabannin kungiyar Likitoci masu bayar da agaji a sassan duniya da ake yi wa lakabi da ‘Doctors Without Boarders’.
A shekarar 2017 ne Hon. Garba Datti Babawo ya fara gabatar da shirin bayar da kiwon lafiya kyauta ga al’ummar azabarsa ta Sabon Gari, musamman don rage musu nauyin da suke fuskanta wajen kula da lafiyarsu da na iyalansu, haka kuma bisa lura da cewa, asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu suna kokarinsu amma wannan kokari nasu bai wadatar ba.
Tunda aka fara a karon farko, al’umma ke tururuwa a duk lokaci da ake gudanar da shirin, inda kwararrun Likitoci ke duba marasa lafiya tare da basu magani a nan take, wadanda lalurarsu kuma take bukatar tiyata sai a garzaya dasu Asibitin Railway inda ake yi musu tiyata ba tare da biyan ko sisi ba.
Kididdiga ya nuna cewa cikin lokacin da aka yi ana gabatar da wannan shiri na bayar da kiwon lafiya kyuta ga al’ummar yankin Sabon Gari dama wasu daga kananan hukumomin da suke makwabtakar karamar Sabon Gari an samu nasarar yi wa al’umma da dama maganin cututtuka daban-daban da suke fama dasu wadanda suka hada da OPD—4,929, masu ciwon ido an ba mutum fiye da 1,996 magani lalurar da suke fama da shi na ido wanda ya hada da wadanda aka ba madubin ido da kuma wadanda aka yi wa tiyata don cire musu cututtuka a cikin idon.
Da yawa daga cikin su sun samu sauki a halin yanzu suna gani tangaras. An kuma gudanar da gwaje-gwaje asibiti do gano cutar da ke cikin jini ga mutane fiye da 2, 210, ta hanyar gwajin ne ake sanin hakikanin cutar da ke cikin jini tare da bayar da maganin da ya dace da cutar, haka kuma an gudanar da binciken kwakwaf (Ultrasound) ga mutane fiye da 282, an kuma ba mutum 700 madubi na musamman na karatu don rage musu matsalolin da suke fuskata wajen karatu, an kuma yi wa mutum 107 aiki a ido don cire musu wata cutar da take damun su wanda a halih yanzu suna nan suna harkokisu ciki walwala yayin da kuma aka yi wa mata 225 aiki a kan abubuwan da suka danganci ciwon su na mata.
Cikin cuttukan da aka bayar da maganinsa ga mutane sun hada da cutar ‘Herniorrhaphies’ inda mutum 156 suka amfana. Mutum 7 masu cutar Myomectomy sun amfana, sa wani mutum 1 mai cutar Cystectomy, shima wani mai cutar Hysterectomy ya amfana yayin da wasu mutum 28 , masu cutar Lumpectomy suka amfana da magunguna daban-daban, an kuma yi wa wasu mata 2 tiyatar cire jariri (C/S), sai wasu mutum 6 masu cutar orchidopedy da mutum 12 masu cutar Ganglionectomy, wadannan kadan daga cikin wadanda suka amfana ke nan da shirin bayar da kiwon lafiya kyauta (Medical Outreach) na Hon. Abubakar Datti Babawo, mamba mai wakiltar mazabar Sabon Gari a majalisar Wakilai ta tarayyar Nijeriya.
A jawabinsa a gangamin da aka yi bayar da kiwon lafiya kyuata ga al’umma karo na 7, Hon Garba Datti Babawo ya fara ne da mika gaisuwa da jinjina ga duykkan wadanda suka samu halartar taron musamman shugaban karamar hukumar Sabon Gari Injiniya Muhammadu Usman (Maku), da sauran manyan baki maza da mata, ya kuma kara da cewa, “A yau ne muke kaddamar da ba da magunguna da ayyuka na cututtuka daban-daban tun daga su Kaba, su Kari da sauran cututtuka su Fibroid da suaransu da aiki na ido da bada gilashi na ido da kuma duba marasa Lafiya gaba daya masu cuta tun daga irinsu Diabetes zuwa irin su sauran dai cututtuka dai gaba daya. Yau za a yi kun ji bayanin da shi likitan talakawa ya yi. Cewa daga yau har zuwa ranar Asabar in Allah ya yarda za a yi wa Mutane akalla dubu bakwai magani, za a basu magunguna kyauta da wanda za a masu aiki na ‘Operation’ da sauransu.
Kamar yadda na fada likitan talakawa, likita ne kuma kwarraren likita wanda yake ‘Consultant’ ne kuma ya zo da kungiya na masana tun daga likitoci zuwa nas-nas zuwa ‘laboratory technicians’ da sauransu’.
Ya kuma kara da cewa ‘’Mune dai muka fara wannan tsari na bayar da tallafin kiwon lafiya ga al’umma yanzu ba Nijeriya na kadai har kasashen waje ana kiran wannan team na doctors on the mobe Africa suna zuwa kasashe daban-daban suna yi wa mutane aiki. Kuma mun ga irin nasarorin da aka samu a wannan karamar hukumar, wannan abu babban makasudin da yasa aka fara yinsa shi ne saboda yanayin da ake ciki. Zaka ga mutane da yawa wasu an rubuta masu maganin na dari biyar ko na dari uku amma basu dashi sai dai su je daki su kira sarautar Allah. Wasu ayyuka ne sun tafi asibitoci amma an gaya masu ba za a iya masu aiki ba sai sun biya kudi ga ciwo na cin mutum, ba kudin wani ba kadaran ma da zai siyar ya bayar ayi mashi wannan magani.
A bisa wannan Dalili muka yi tunanin cewa ta yaya tunda kullum mu ake kawo ma koke ta ya za mu iya taimakawa mutane musamman marasa galihu wanda ba za su iya zuwa asibiti su biya kudin aikin nan ba.
Mun san akwai wanda suka je na farko matar da aka rubuta mata kudi miliyan daya da dubu dari hudu basu dashi sun zo nan a yi masu wannan aiki kyauta. Akwai mai dubu dari takwas, dubu dari hudu da dubbai ba adadi ana zuwa nan kuma cikin ikon Allah ana masu aikin nan ana samun nasara. Toh wannan abu Babban abun farin ciki ne a gare mu a wannan yanayi kamar yadda suka yi bayani mai ba gwamna shawara da wanda ya yi muna dai kan gaba ta siyasa amma dai harkar lafiya mu inda muke a nan bama sa siyasa a ciki.
Saboda duk wanda yazo nan mun san gajiyye ne kuma yana neman taimako mai lalura ne kawai zai zo”
Daga nan ya yi kira ga al’ummar da ke tururywa don amfana da wannan shirin da su natsu tare da bayar da dukkan goyon bayan da suka kamata ga jami’an da ke tafiyar da shirin don a samu ganin kowa ba tare da matsala ba.
A masa jawabin, shugaban tawagar Likitocin da ke gudanar da shirin Dakta Haruna Kibu ya fara ne da cewa, ‘’Muna yi wa Hon. Garba Datti godiya, domin wannan shiri ne na bakwai wanda Allah ya sa ya kawo mu nan garin Zariya muna yi wa jama’arsa aiki.
Ba ‘yan majalisa duka suka iya yin irin wannan kokari ba, wannan yana nuna kwarewarsa ne da kuma damuwarsa da lafiyar al’ummarsa. Kuma yana tunanin ku a kulli yaumin, yana tunanin rashin lafiyar ku.
Ya kara da cewa, yana da wuya in mutum ya samu rashin lafiya bashi da kudin zuwa asibiti ya samu ya yi jinya. Kenan Hon. Garba Datti ya samar da wannan Shirin ne don taimakawa al’ummarsa samun magunguna da kulawar likitoci a cikin sauki, wannan babbar lamari, ya kuma kamata su gode wa Allah da ya basu irin wannan shugaban.
Daga karshe ya mika godiyarsa ga Hon Gatrba Datti Babawo a kan damar da ya bashi tare da tawagarsa na gudanar da wannan aiki a karamar hukumar Sabon Gari, ya kuma nemi al’umma su yi amfani magungunan da aka basu yadda ya kamata.
Wasu da dama da wakilimu ya tattauana da su sun nuna godiyarsu ga Hon Garba Datti Babawo a bisa wannan alhairin da ya kawo musu yankin Saboin Gari sun bukaci a cigaba da kawo shirin akai-akai.
Malam Shehu Alfa da ke hayin Dogo Samaru Zariya wanda aka yi aiki don cire cutar Kaba, ya ce, “Ina godiya ga Hon. Datti Babawo da ya samar da wannan shiri na bayar da magani kyauta, da ba don shi ba, da har yanzu ina fama da lalurar, na gode kwarai da gaske” in ji shi.
Hon. Datti Babawo ya gabatar da ayyukan raya kara da kula da harkokin al’umma da dama a sassan mazabarsa ta Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.