Dakarun Sojin Nijeriya sun kama masu rajin kafa kasar Yarbawa guda tara, wadanda suka kai hari sakatariyar Jihar Oyo da ke yankin Agodi a Ibadan, a ranar Asabar.Â
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar, ta ce mutanen na sanye da kakin sojoji na kasashen waje, sannan dauke da muggan makamai.
- Ko Hana Fina-finan Daba Zai Rage Aikata Laifukan Daba A Kano?
- Abubuwan Da Za A Rika Tuna Saratu Gidado Da Su A Fagen Fim
Sanarwar ta ce sun zo sakatariyar ne a cikin motoci kirar bas da babura.
Sai dai ya ce sojoji sun yi artabu da su, lamarin da ya kai ga musayar wuta tare da tarwatsa su.
Ya ce: “Bayan yin artabu da sojoji, masu rajin kafa kasar Yarabawa sun yi ta kansu, inda aka tarwatsa su.
“An kama wasu daga cikin wadanda suka kai harin tare da kwato makamai.”
Janar Nwachukwu, ya ce dakarun soji sun yi kokarin kwantar da hankali tare da daidaita lamura a yankin.
Ya tabbatar wa jama’a cewa an dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaro a yankin.
Ya kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan, tare da kai rahoton duk mutumin da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro da suka dace.
Ya kara da cewa, “Tsaro da tabbatar da zaman lafiyar ‘yan kasa shi ne abin da muka sa gaba,” in ji shi
Ga hotunan wadanda aka kama a kasa: