Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya jaddada cewa tsarin dimokuradiyyar Turawan yamma da kasashen Afirka suka kwaikwaya bai karbe su ba, inda ya bayar da hujjojinsa kan fadar haka.
Da farko Obasanjo ya ce dimokuradiyyar turawan ba ta dace da yanayin tarihi, al’adu da kabilun mutanen yammacin Afirka ba.
- An Gudanar Da Bikin Reel Africa A Birnin Shanghai
- Ya Zuwa Karshen Shekarar Bara Tsayin Manyan Titunan Mota Na Kasar Sin Ya Kai Kilomita 177,000
Haka nan, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa salon dimokuradiyyar kasashen yammacin duniya ya gaza a Nahiyar Afirka domin ba ta la’akari da ra’ayin mafi yawan jama’a.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin a wani babban taron tuntuba kan sake tunanin dimokuradiyyar Turawan yamma a Afirka, wanda ya gudana a Abeokuta, Babban Birnin Jihar Ogun.
Obasanjo, wanda ya kira taron, ya kuma siffanta dimokaradiyyar turawan na yamma a matsayin gwamnatin mutane kalilan da ke mulkan mutane masu dimbin yawa, kuma wadannan tsirarun mutane ne kawai wakilan wasu daga cikin jama’a, amma ba wakilan al’umma ba.
Ya ba da shawarar a sauya dimokuradiyyar Turawan yamma a kasashen Afirka.
A cewarsa, kasashen Afirka ba su da wata alaka wajen tafiyar da tsarin gwamnati wanda ba su da hannu a cikinsa.
Obasanjo ya ce, “Rauni da gazawar dimokuradiyyar Turawan yamma dai ya kunshi yadda ake aiwatar da ita ya saba da al’adun kasashen Afirka.
“Da zarar ka tashi wakiltar mutane, za ka fara fuskantar kalubale da matsaloli. Ga wadanda suka ayyanata a matsayin mulkin mafi rinjaye, shin ya kamata a yi watsi da tsiraru.?
“A takaice, muna da tsarin gwamnati wanda ba mu da hannun wajen tsarawa da kuma aiwatarwa, bai kamata mu ci gaba da amfani da shi ba, alhalin mun san ba ya mana aiki.
“Wadanda suka kawo mana shi a yanzu suna kokwanton sahihancinsa da suka kirkira, a yanzu kuma bai dace ba idan har ba za a gyara ba.
“Muhimmancin kowane tsarin gwamnati shi ne walwala da jin dadin al’ummar kasa.
“A nan, dole ne mu yi duba yanayin kwazon dimokuradiyyar Turawan yamma da suka gadar mana tun lokacin mulkin mallaka.
“Mun taro a nan ne don yin tunani a matsayinmu na jagororin ilimi da kuma na siyasa wajen fitar da matsaya kan dimokuradiyyar Turawan yamma.”