Hukumar tace Fina-finai da dab’i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El Mustapha ta bayar da umarnin rufe gidajen gala da sauran wuraren wasanni a jihar Kano.
Umarnin hakan na cikin wata takarda da jami’in yada labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Suleiman ya fitar, inda yace an yi hakan ne saboda gabatowar azumin watan Ramadan.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Duba Ƙarin Farashin Wutar Lantarki
- Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikata
Malam Abdullahi ya bukaci dukkan mahukuntan gidajen gala a jihar Kano da su tabbatar da sun bi wannan umarni, inda ya tabbatar da cewar, an tanadi hukunci mai tsauri akan duk wanda aka samu da laifin taka dokar.
Hakazalika, an hana duk wani dan wasan gala ci gaba da zama a gidan gala har zuwa 1 ga watan Shawwal na wannan shekarar, a karshe ya yi kira ga shugabannin kungiyar masu gidajen gala da su saka idanu wajen ganin an cimma nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp