Daga Sulaiman Ibrahim,
Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa kura da ta kunno kai a jamhuriyar Nijar da kuma yammacin Chadi na iya kawo cikas ga ayyukan jiragen sama a Nijeriya, musamman a sassan arewacin kasar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a ranar Alhamis din nan daruruwan fasinjoji sun taru na tsawon sa’o’i a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport (NAIA), Abuja, amma yanayin hazon ya hana kamfanonin jiragen saman ba jiragen daman tashi.
Dakin tashi da saukar jiragen sama na Abuja ya cika makil da fasinjojin da ke cike da takaici wadanda suka yi zugum suna jiran ikon Allah