Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Nijeriya (NCoS) ta bayyana cewa za ta ci gaba da neman fursunonin 69 kwanaki uku bayan da kungiyar ‘Yan ta’adda ta ISWAP ta kai hari gidan gyaren hali na Kuje da ke Abuja a ranar Talata, 5 ga Yuli, 2022.
An kubutar da daruruwan fursunoni daga wurin bayan harin da kungiyar ta’addancin ta kai.
- Harin Gidan Yarin Kuje: Buhari Ya Gana Da Hafsoshin Tsaron Nijeriya
- Harin Kuje Da Tawagar Buhari: Ya Kamata A Sauya Shugabannin Tsaro – Alhaji Ibrahim
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a safiyar ranar Juma’a, ta bayyana fursunoni 69 da ke fuskantar shari’a kan ta’addanci da ake nema ruwa a jallo, inda ta bukaci jama’a da su bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga sake kama su.
Sanarwar ta kuma ƙunshi hotuna, sunaye da sauran cikakkun bayanai game da masu gudun hijira 69.
“Waɗannan su ne fuskoki da sunayen fursunonin da ke da shari’ar BOKO HARAM / TA’ADDANCI da suka tsere daga gidan yarin Kuje a harin gidan yari a ranar 5 ga Yuli, 2022.
“Idan ka ga daya daga cikin wadannan mutane, ko kuma kana da bayanai masu amfani da za su kai ga sake kama su, to ka kira 07000099999, 09060004598 ko 08075050006 ko kuma duk wata hukumar tsaro da ke kusa da ku.
Muna ba da garantin ɓoye bayananku, ” cewar sanarwar.
Hukumar ta kuma samar da shafin yanar gizon, www.corrections.gov.ng/escapees, inda za a iya duba duk waɗanda suka tsere daga gidan yarin Kuje.