Hukumar INEC Ta Ce Ba A Kammala Zaben Gwamnan Anambra Ba

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana zaben gwamna na jihar Anambra a matsayin wanda ba a kammala ba, wato ‘Inconclusive’ kenan a turance. Hakan ya biyo bayan rashin yin zabe a karamar hukumar Ihiala, wacce wakilan jam’iyyar PDP da na APC suka ki sanya hannu a sakamakon zaben.

A sakamakon da yake hannu, wacce hukumar zaben ta bayyana dan takarar jam’iyyar APGA Farfesa Charles Soludo ne a kan gaba da kuri’a 103,946, sai dan takarar jam’iyyar PDP Valentine Ozigbo mai kuri’a 51,322 sai Andy Uba na jam’iyyar APC mai biye mishi da kuri’a 42,942. Ifeanyi Uba shine dan takara na hudu mai kuri’a 20,917.

Hukumar ta bayyana cewa za ta sake gudanar da zabe a karamar hukumar Ihiala wacce ake tababar sakamakon zaben ta, kawo yanzu hukumar ta bayyana yaushe zata gudanar da zaben. Inda Baturiyar zabe Florence Obi ta bayyana ranar Talata 9 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a gudanar da zaben.

Exit mobile version