Khalid Idris Doya" />

Hukumar Inshorar Lafiya Ta Sauya Cibiyoyin Lafiya Hudu A Bauchi

Hukumar Inshoran lafiya ta kasa (NHIS) ta tantance gami da bayar da lasisi ga cibiyoyin kiwon lafiya hudu a jihar Bauchi da zimmar kara kusanto da cibiyoyin kiwon lafiya zuwa kusa da al’umma.
Bayan nan, an kuma daukaka matsayin wasu cibiyoyin lafiya hudu, a gefe guda kuma aka kori wasu cibiyoyin lafiya hudu daga cikin shirin gaba daya a sakamakon gazawarsu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labarai dauke da sanya hanun Ko’odinetan hukumar Insholan lafiya (NHIS) a jihar Bauchi, Alhaji
Sani Garba Affa wanda ya raba wa ‘yan jarida a Bauchi.
Hukumar ta bayyana cewar wannan matakin na dauke ne a cikin shirinta na tabbatar da kai sha’anin ilimi zuwa mataki da ya dace daidai da matakin kasa da kasa, da kuma tabbatar da samar da horo ga wadanda suka kauce wa ka’idar shirin hukumar.
Hukumar ta ce wannan karin cibiyoyin lafiya hudun shine ya kawo adadin cibiyoyin lafiya guda 53 da suke cikin shirin na Inshoran Lafiya a jihar Bauchi.
Haka zalika, NHIS ta kuma kara daukaka matsayin wasu cibiyoyin jihar guda hudu daga karamin aji zuwa babban aji a sakamakon kokarinsu kan shirin, wadanda suka samu karin matsayin su ne asibitin koyarwa ta ATBU ‘Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital’, Asibitin kwararru da ke Bachi ‘Bauchi State Specialist Hospital’, Aibitin Reeme, da kuma asibitin jinya na gwamnatin tarayya da ke Azare.
Ya bayyana cewar daga cikin cibiyoyin kiwon lafiyan da suka samu sahalewar sun hada da; ‘261 Nigeria Air Force’ Asibitin rundunar sojin sama ta kasa da ke Bauchi, Nagari Clinic, Asibitin As-Salam da kuma Medical Centre da ke Azare a cikin karamar hukumar Katagum.
Sanarwar ta kara da cewa a hakan duk na daga cikin kokarin shirin na NHIS don tabbatar da inganta kiwon lafiya a kasar nan.
Baya ga nan kuma; sanarwar ta shaida cewar hukumar Inshoran lafiyar ta kuma cire wasu cibiyoyin kiwon lafiya guda hudu da suke Bauchi a karkashin shirin nata, a bisa gazawarsu; cibiyoyin kiwon lafiyar da aka cire a cikin tsarin Inshoran lafiyan sun kunshi; Asibitin da ke cikin jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Yalwa a cikin Bauchi, Peoples Clinic, Asibitin Alwadata da kuma karamin asibitin mai suna Under 5, dukkaninsu an cire su daga cikin shirin.
Sani Garba Affa ya kara da cewa, daukan wannan matakin ya biyo bayan wani aiki da NHIS ta gudanar a cibiyoyin lafiya da suke fadin kasar nan domin gano yadda suke da matakin da ya dace a bar su a ciki.
Sanarwar NHIS ta ce

Exit mobile version