Connect with us

LABARAI

Hukumar JAMB Ta kayyade Maki 160 A Matsayin Shiga Jami’a A 2020/2021

Published

on

A wata tattaunawa da Hukumar kula da jarabawar tsallake siradin shiga makarantun Jami’o’i da makarantar gaba da Sakandare, JAMB, wanda ta yi da sauran Hukumomi da suka hada da Shugabannin makarantun Jami’a, da kuma Babban Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, da sauran kungiyoyi da suka hada da shugaban fanni masu yi wa kasa hidima (NYSC) da sauran ma’aikatan ta, JAMB ta sanar da makin 160 a matsayin mafi karanci da idan dalibi ya kai zai iya samun damar zuwa Jami’a a shekarar karatu ta 2010/2021.

Taron ya gudana ne a ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2020, a babban ofishin Hukumar JAMB da ke Abuja.

Shugaban Hukumar ta JAMB, Farfesa Is’hak Oloyede, ya ce a yayin gudanar da taron, “an kayyade makin 160 zuwa sama, shi ne makin na samun dama zuwa Jami’a, makin 100 zuwa sama shi ne damar zuwa karatun Kwalejin Ilimi, da sauran Makaratun Diploma”. Ya kara da cewa wannan dokar ta biyo bayan zabe da ya gudana game da makarantu suka yi.

Har ila yau ya ce, babu wata Jami’a da aka ba ta damar daukan dalibi wanda makin jarabawar sa ta JAMB bai kai 160 ba. Kuma ya kara da cewa, ba iya wannan ba, wasu makaratun suna wata jarabawar tsallake siradi bayan JAMB din, wanda aka kira da (Post UTME).

Daga cikin jawaban na Shugaban, ya ce babu dalibin da zai samu shiga Jami’a da maki kasa da 160, bayan matsaya na zabe da makarantu suka yi. Makarantun da suka zabi 160 a matsayin shi ne kayadajjen makin shiga Jami’a yawan su ya kai 210, yayin da kuma wadanda suka ce duk abin da ya sauka kasa da maki 210, su kuma yawan su 209″.

Ya kara da cewa, gaba daya Jami’o’i da suke neman kasa da 160 ba zai samu karbuwa ba, sai dai daga 160 zuwa sama, haka ma Makarantun Kimiyya da Fasaha ‘Polytechnic’, da Kwalejin Iilimi, kowacce Makaranta za ta bi abin da aka fada ne. Babu wani gurbi a bayan fage, kowane gurbi za a bayar ne a Hukumance karkashun ikon CAPS. Duk makarantar da ta saba wa dokor tsarin wannan taron za mata hukunci. Ana sa ran za a fara sanar da daukar sabbin daliban a 21 ga watan Ogustan 2020.

Sannan kuma kowace makarantu masu gudanar da jarabawar Post UTME, kar su sanya kudin yin rejistar ya haura N2000, har da lissafin cajin da banki zai yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: