Hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta kwace wasu rumfunan ajiya 10 dauke da kayan abinci iri-iri a yankin Dawanau da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar.
Shugaban hukumar, Muhyi Magaji, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kwace rumbunan da ke kasuwar hatsi ta kasa da kasa ta Dawanau da kasuwar Singa da kuma kasuwar Kwari a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce babu inda aka samu masu irin wadannan ma’ajiyar a yayin gudanar da aikin amma wadanda aka bude sun cika makil da kayayyaki da suka hada da taliya da shinkafa da sukari da sauran kayan abinci.
“An bayar da sanarwar cewa masu kayan su kai kan su hukumar don kare tuhumar da ake yi musu a gaban kotun shari’a kan laifukan da suka aikata ba bisa ka’ida ba. Cewar Muhuyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp