Abdullahi Sheme" />

Hukumar Kare Hadura Reshen Shiyyar Funtua Ta Ja Kunnen Masu Keke Napep

Hukumar kare hadura ta kasa reshen shiyyar Funtuwa (FRSC) ta ja kunne masu haya da Keke Napep, wadanda a ke kira da ’yar kurkura.
Jan kunnen ya fito ne daga bakin shugaban kare hadura na kasa reshen shiyyar Funtuwa, I. M. Lawal, ta bakin mataimakinshi, A. A Bello, a lokacin da hukumar ke kewayen wayar da kan direbobin kungiyar a Funtuwa a jihar Katsina.
A ranar Larabar nan ne hukumar kare hadura ta kasa ta kira taron direbobin kungiyar, domin gabatar da dokokin ga direbobin su ne an hana duk wani direba sa manyan lasifika da rikoda da kuma hana saka labule da samar da gilashi mai duhu (tintet) a cikin kekunan NAPEP dinsu.
Doka ta fara aiki nan take kuma hukumar za ta fara kama duk wanda yaki bin doka, domin hukunta shi, inji A. A. Bello.
Mataimakin shugaban hukumar ya cigaba da cewar, wannan doka ta fito ne daga gwamnatin jihar Katsina hade da hukumarsu, ya na mai cewa, ya zama wajibi ganin yadda direbobin kungiyar su rika hana sauran matafiya a cikin garin Funtuwa jin yanayin gari, saboda yawan sanya kade-kade a cikin kekunansu na hanya da dai sauran wasu laifin da direbobin ke aikatawa.
A nashi jawabin shugaban kungiyar direbobin Keke Napep na kasa reshen shiyyar Funtuwa, Alhaji Kabir Yusuf Unguwar Wanzamai Funtuwa, ya gode wa hukumar shiyyar Funtuwa, saboda irin bitar da su ke yi wa mambobinsu a lokatu daban-daban.
Ya ce, su na da kyakykyawar fahimta tsakaninsu da hukumar, ya na mai kira ga shugaban hukumar Funtua Malam Lawal Sani Matazu, domin ya bai wa kungiyarsu filin da za su gina ofishinsu na dindindin. Ya ce, ofishinsu na yanzu haya su ke yi.
A lokacin da wakilin LEADERSHIP A YAU ya tambayi Shugaba Alhaji Kabir Yusuf yadda kungiyar ke samun kudin shiga, ya ce, su na samun kudin shiga ta hanyar samar da rasiti na Naira 50, don tafiyar da kungiyar, ya ce, su na da ma’aikata 14 masu aiki a ofishin kungiyar, ya ce shi ne shugaban kungiyar na kananan hukumomi 11 na yankin Funtuwa kuma su na da mambobin kungiyar kusan mutum 2,000, wadanda su ka yi rijista da kungiyar.
Shugaban ya yi kira da ’yan kungiyar da su bi doka da oda, kuma ya ce, direbobin su kula da irin fasinjan da su ke dauka kuma idan fasinjoji sun manta kayansu su daure su rika kawo wa ofishin kungiya, domin idan masu kayan sun yi cigiya su rika ba su.
Kuma ya ce, su zama mutanen kirki, su yi tuki da kula, domin kekunan NAPEP din sun yi yawa a cikin garin Funtuwa; dole ne direbobin su rika daukar fasinjojin Bakori da Mairuwa da karamar hukumar Faskari da Mahuta da karamar hukumar dandume da dai sauran wurare.
Sannan kuma ya ce, su na godiya ga gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari kan yadda a ke taimakon kungiyoyi.
Daga karshe shugaban hukumar kare hadura ta kasa shiyyar Funtuwa ya yi kira ga al’ummar yankin su ba wa hukumarshi hadin kai da taimakon hukumar, don cigaban yankin domin kare hadura da hukamar don cigaban yankin domin kare hadura da bin doka da oda a yankin da ma kasa bakidaya.

Exit mobile version