Hukumar kula da aikin makaurata ta kasar Sin ta tsai da kudurin kara daidaita manufofin ba da iznin shigo kasar da matakan shigo kasar daga ketare daga ranar 15 ga wata, a kokarin biyan bukatun dakile da kandagarkin cutar COVID-19 da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da ma ba da sauki ga cudanya a tsakanin Sin da kasashen waje.
Matakan kuwa da suka hada da amince shigowar baki cikin kasar Sin, wadanda suka samu bizar da aka sa hannu a kai kafin ranar 28 ga watan Maris din shekarar 2020, yayin da tabbatar da lokacin amfanin bizar yadda ya kamata.
Kana za a dauki matakan amincewa da baki su shigo lardin Hainan ko birnin Shanghai ta hanyar daukar jirgin ruwa iri na yawon shakatawa ba tare da biza ba.
Sannan baki wadanda za su shiga lardin Guangdong cikin kungiya daga yankunan Hong Kong da Macao, da ma baki masu yawon bude ido daga kasashen ASEAN da za su shigo birnin Guilin na jihar Guangxi cikin kungiya ba tare da biza ba. (Kande Gao)