Shugaban Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), Kanar Hameed Ali mai ritaya, ya ce an kori sama da jami’ai 2,000 a cikin shekaru 7 da suka gabata saboda cin hanci da rashawa.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a taro na 53 na fadar shugaban kasa da manema labarai na fadar ke shirya wa, a Abuja.
Hameed Ali, ya ce wasu daga cikin wadanda aka kora, an gurfanar da su a gaban kotu tare da daure su a gidan yari saboda a cewarsa, a gwamnatinsa sam bai yarda da cin hanci da rashawa ba.
Kanar Hameed ya ce, an samu da yawa daga cikin wadanda aka kora din suna tauye wa Hukumar kudaden shiga, musamman a kudaden da ya kamata a biya na motocin da ake shigowa da su daga waje.
Ya ce galibin masu ababen hawa suna da laifin rashin bayyana hakikanin shekarar da aka kera Motocin da suke shigowa da su, motocin da aka kera shekarar 2022 sai su maida ita a matsayin ‘yar 2015 domin kada su biya hakkin da ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp