Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wasu mutane 85 da take zargi da ta’ammuli da miyagun kwayoyi a wani gidan casun dare da ke Kano a ranar Litinin.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano, Abubakar Idris-Ahmad, kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, ya ce kamen ya biyo bayan korafe-korafen da aka kai kan yawaitar masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi a gidan casun.
Ya ce, masu gidan casun ne suka shigar da korafe-korafen ga hukumar kan yadda aka mayar da gidan wurin shan miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa, wadanda aka cafken sun hada da maza 55 da mata 30, daga cikin kwayoyin da aka kama a tare da su akwai tabar wiwi da sauran kwayoyi.
Mista Idris-Ahmad ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton ayyukan da suka shafi ta’ammuli da muggan kwayoyi ga hukumar domin hukumar ba za ta bar wata maboyar masu safarar miyagun kwayoyi a jihar ba.