A ranar 18 zuwa ranar 19 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai hallarci taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya da za a gunadar a birnin Xi’an dake lardin Shaanxi tare da shugabannin kasashen tsakiyar Asiya biyar da suka hada da Kazakhstan da Uzbekistan.
Wannan taron koli shi ne babban taron diplomassiya na farko da Sin za ta yi a bana, wanda kuma shi ne taron koli na farko da shugabannin kasashen shida za su gudanar a zahiri tun bayan kulla huldar diplomassiya yau shekaru 31 da suka gabata.
“Na fito daga lardin Shaanxi na kasar Sin, wanda shi ne asalin tsohuwar hanyar siliki.” A watan Satumba na shekarar 2013, shugaba Xi ya fara ziyararsa ta farko a tsakiyar Asiya. Yayin da ya gabatar da jawabi a jami’ar Nazarbayev dake Kazakhstan, ya waiwayi tsohuwar hanyar siliki mai tarihin shekaru fiye da 2000 da ta hada nahiyoyin Turai da Asiya, kuma ya ba da darasin da tsohuwar hanyar siliki ta baiwa zuri’ar da ta biyo baya.
A cikin shekaru goma da suka gabata, manyan jami’an Sin da kasashe biyar na tsakiyar Asiya sun yi mu’ammala sosai, inda shugaba Xi ya kai ziyara yankin har sau bakwai.
A cikin taron kolin Sin da tsakiyar Asiya da za a gudanar nan ba da dadewa ba, Sin da kasashen biyar za su sake nuna ci gaban abotarsu mai inganci ga kasa da kasa, kuma dalilin da ya sa shi ne bangarorin biyu sun gane sirrin samun nasara. Kamar yadda shugaba Xi ya ce, Sirrin samun nasara game da dangantakar da Sin da kasashe biyar na tsakiyar Asiya suka gudanar cikin shekaru 30 da suka gabata, shi ne mutunta juna, tabbatar da kyakkyawar makwabtaka, hadin kai, cin moriyar juna da kuma samun nasara tare. (Safiyah Ma)