Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta sanar da cewa ta samu nasarar tarwatsa wasu dillalan safara da sayar da miyagun kwayoyi da ke aiki a jihohin Kano da Abuja.
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce, an samu nasarar tarwatsa wata kungiyar masu safarar hodar iblis da tabar heroin tare da kama Onyeka Uba mai shekaru 42 a unguwar Sabon Gari a jihar Kano.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 3 Da Ake Zargi Da Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane A Bauchi
- Buhun Taki Miliyan 2 Da Biliyan 100 Da CBN Ya Bayar Zai Daidaita Farashin Abinci -Kyari
Babafemi ya bayyana cewa, an kwato kilo 1.805 na haramtattun abubuwa daga hannun wanda ake zargin a ranar Litinin 18 ga watan Maris.
An kuma kama wani wanda ake zargi mai suna Ubale Sani mai shekaru 49 da tabar wiwi mai nauyin kilo 51.5 a unguwar Chiromawa da ke Kano.
Hakazalika, jami’an rundunar ta NDLEA, sun kuma dakile ayyukan wata kungiyar ta’ammali da hodar Iblis a Abuja a karshen mako tare da kama wasu shugabannin kungiyar guda uku.