Hukumar NEMA Ta Fara Aiki Don Takaita Faruwar Annoba 

Hukumar dake kula da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta sanar da wani shiri da ta fara don takaita afkuwar annoba a kasa gaba daya, babban jami’in hukumar na jihar Imo da Abiya, Mista Evans Ugoh ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Owerri na jihar Imo a yau Litinin.

Cikin shirye-shiryen da hukumar take yi akwai samar da kafar sadarwa mai inganci sosai, sannan hukumar za ta tabbatar da ta samar da irin wannan kafar mai karfi tare da sauran hukumomi don magance faruwar annoba a jihohin kasar nan gaba daya.

Jami’in ya bayyana rashin wadatattun kayan aiki a matsayin manyan matsaloli da suke fuskantar hukumar wajen gudanar da aikin ta yadda ya dace, inda ya bukaci da adinga samarwa wadannan hukumomin da suka dace, saboda ta hakan ne kawai hukumomin zasu gudanar da ayyukansu.

Ugoh ya bayyana yadda hukumar NEMA ta gudanar da ayyukan jin kai a alokacin da aka samu annoba a jihohin Imo da Abiya, sannan hukumar ta samu nasarar samar wa da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa kayan agaji a karamar hukumar Ohaji-Egbema dake jihar Imo a cikin shekarar 2018.

Exit mobile version