Kwantirolan hukumar kula da shige da fice (NIS) dake kula da iyakar Mfum da daura da Ikom a cikin jihar Ribas, Mista Ndubuisi Eneregbu ya tabbatar da cewa, Jami’an rundunar sun kama mutum uku da take zargin masu safarar makamai ne.Â
Ndubuisi wanda ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar a garin Kalaba,y sanar da cewa, iyakar ta Mfum na daya daga cikin iyakokin da ake yin safarar motoci na kasa da kasa.
Eneregbu ya ce wadanda ake zargin a cikin su akwai ‘yan Nijeriya biyu sai wani dan kasar Kamaru.
Ya ce tuni an mika su ga hukumar ‘yansanda na karamar hukumar Etung domin Cigaba da bincike.