Rundunar ‘yansanda ta NSCDC reshen jihar Kano ta dakile wani yunkurin fashi a Unguwar Fulani da ke karamar hukumar Kumbotso bayan amsa kiran gaggawa.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar a jihar, SC Ibrahim Abdullahi, ya fitar, ta bayyana cewa, amsa kiran gaggawa da jami’an NSCDC daga ofishin Kumbotso suka yi, ya kai ga kama wasu mutane 9 da ake zargi da hannu a yunkurin fashin da aka dakile.
- Yadda Sha’anin Noman Abarba Ke Taimakawa Kyautata Zaman Rayuwar Mazauna Wasu Kauyuka A Kasar Sin
- Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Yawan Jima’i A Benuwe
Wadanda ake zargin, sun hada da Abba Nasiru Adamu, Ibrahim Adamu, Hassan Sulaiman, Basiru Aliyu, Hashimu Ibrahim, Umar Hudu Hassan, Shamsu Haruna, Ibrahim Abubakar, da Mudassir Hassan Dahiru.
SC Abdullahi ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun shirya yin fashin ne a wani kamfani da ke cikin Unguwar masana’anta ta Challawa a jihar.