Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Hukumar Shige Da Fice Ta Kaddamar Da Jami’anta 396 Da Ta Horas 

Hukumar Kula da Shige da Ficen Kasa (NIS), ta kaddamar da wasu jami’anta da ta horas a cikin ayyukanta a wani biki na tarihi da ya gudana a Makarantar Horas da Jami’an Shige da Fice ta Kano.

Bikin ya samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan, ciki har da shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasar Ghana, Kwame Asuah Takyi, da babban bakon da ya duba yanayin horon da aka bai wa jami’an da aka kaddamar, shugaban hafsoshin sojin Nijeriya, Janar Olanishakin wanda Air Vice Marshal Balogun ya wakilta. Har ila yau, akwai babbar sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Barista Georgina Eukharia, da kwamishinonin hukumar gudanarwar hukumomin rundunar tsaron fararen hula, kashe gobara, shige da fice da gidajen yari, Manjo Janar Bassey mai ritaya da ACG Ado Jafaru mai ritaya, wadanda baki daya suka shaida bikin a kwaryar birnin Kano.

Jami’an da aka kaddamar din za a rarraba su a sassan ayyukan hukumar ta shige da fice daban-daban da suka kunshi kula da kan iyakoki ta na’urar zamani, fasahar sadarwa ta zamani, yi wa baki masu shigowa kasa rajista ta na’ura da sauran sassan da ke aiki da makami na hukumar.

Da yake jawabi a wurin bikin, babban hafsan hafsoshin sojin kasar nan, Janar Olanishakin, ya bukaci jami’an da aka yaye su nuna kwarewa wurin gudanar da ayyukansu na kula da shige da fice da kuma sauran abubuwan da suka shafi tsaron kasa, kana ya yaba wa shugaban NIS, Muhammad Babandede bisa gagarumar nasarar da hukumarsa ke samu wurin gudanar da ayyukanta.

A nashi bangaren, shugaban NIS, Muhammad Babandede ya gargadi jami’an da aka kaddamar su guji neman kamun kafa don tura su wurin da suke so su yi aiki da sauran dabi’un da suka saba wa ka’idar aiki. Wakazalika, shi ma shugaban hukumar shige da fice ta Kasar Ghana, Kwame Asuah Takyi, ya jinjina wa hukumar shige da fice ta Nijeriya, kana ya yi alkawarin yin aiki kafada-da-kafada da ita domin samun ci gaba.

 

Exit mobile version